Watakila Kotun Koli ta Yanke Hukunci a Shari’ar Zaben Gwamnan Kano Nan da Kwana 5

Watakila Kotun Koli ta Yanke Hukunci a Shari’ar Zaben Gwamnan Kano Nan da Kwana 5

  • Kotun koli za ta yi zama domin a warware shari’o'in zaben gwamnonin jihohi da yawa a makon nan
  • Akwai kararrakin da yanzu za a fara zama a game da su, ba za a rasa wanda za a yanke hukunci ba
  • A karshen mako ake tunani APC, NNPP, PDP da LP za su san makomarsu a jihohin Kano da Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kotun koli ta shirya sauraron korafin shari’o’in zaben gwamnonin jihohi 21 a wannan mako da aka shiga a Najeriya.

Tsakanin Litinin zuwa Alhamis, The Nation ta ce za a saurari karar zaben gwamna na jihohin Ebonyi, Filato, Delta da Adamawa.

Gawuna Abba Kano
Kano: Abba Kabir Yusuf, Nasiru Gawuna Hoto: @Kyusufabba, @AbubakarmusaDK1
Asali: Twitter

Sauran kararrakin da za a fara saurara a babban kotun kasar a makon nan sun hada da na Abia, Ogun, Kuros Ribas da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: APC sun hango nasara, 'shirin' rantsar da Gawuna ya kankama a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukunci shari'ar zaben 2023 a kotun koli

Bayan sauraron kara a karon farko, akwai shari’o’in takarar gwamna da ake sa ran a yanke hukunci a kan su a karshen mako.

Rahoton ya ce babu mamaki a ranar Juma’a, alkalan kotun koli su zartar da hukunci a kan shari’ar zaben gwamnan Kano da Legas.

Kafin nan an saurari karar zaben Kano da Legas da aka yi a 2023, ana zaman jiran lokacin da kotun koli za tayi wa jam’iyyu hukunci.

Kotun koli: Shari'ar Kano da Legas

A Legas, APC ta samu nasara a kotun korafin zabe da na daukaka kara a kan LP da PDP.

Lamarin ya bambanta a Kano inda jam’iyyar APC mai adawa tayi nasara a duka kananan kotu kan NNPP da ta karbi mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Jerin ƙararraki 21 da kotun koli zata saurara da yanke hukunci kan zaben wasu gwamnoni a mako 1 tal

Sauraron shari'o'in da ke kotun koli

A ranar Talata za a saurari karan da PDP da INEC su ka daukaka a Filato da kuma karar SDP, APC da APC a zaben gwamnan Delta.

Washegari alkalan kotun koli za su fara zaman shari’ar gwamna Ahmadu Fintiri a Adamawa wanda ya yi galaba a kotunan baya.

Zuwa Alhamis, za a saurari shari’o’in PDP, APC, YPP, NNPP da hukumar INEC a kan zabukan Abia, Ogun, Kuros Riba da Akwa Ibom.

Fatan nasarar Abba Kabir Yusuf a Kano

Ana da labarin ana jiran hukuncin da za a zartar wanda zai kawo karshen takarar Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf a jihar Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano wanda NNPP ta ke da rinjaye tayi wa Abba Kabir Yusuf fatan yin nasara da ya cika shekara 61 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng