Da Alamu Ganduje Ya Shiga da Kafar Dama, Ya Sake Karbar Sanata Kuma Tsohon Minista Zuwa APC
- Sanata Emmanuel Ewuga ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a yau Asabar 6 ga watan Janairu a jihar Nasarawa
- Shugaban jam'iyyar, Dakta Abdullahi Ganduje shi ya karbi sanatan da wasu jiga-jigai a Lafia babban birnin jihar Nasarawa
- Sanatan wanda tsohon karamin Ministan Abuja ne ya bayyana dalilan da suka saka shi sauya sheka zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Nasarawa - Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya sake karbar wasu sabbin tuba zuwa jami'yyar a jihar Nasarawa.
Ganduje ya karbi Sanata Emmanuel Ewuga wanda tsohon karamin Ministan Abuja ne da wasu mutane, cewar Tribune.
Su waye suka sauya sheka zuwa APC?
Yayin bikin a yau Asabar 6 ga watan Janairu a Lafia, Ganduje ya ce Sanatan babban kadara ne ga jam'iyyar, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a karkashin mulkinsa, zai yi mai yiyuwa don ganin ya sasanta tsakani musamman ga wadanda suka bar jami'yyar a baya.
Ya kara da cewa hakan shi zai ba su damar hada kai da kuma samun nasara a zabuka masu zuwa nan gaba.
Shugaban jam'iyyar ya yi musu alkawarin basu dama kamar sauran 'yan jami'yyar don ba da tasu gudunmawa a jam'iyyar.
Wane martani Gwamna Sule ya yi?
Har ila yau, ya kuma bayyana cewa jami'yyar ta yi wani tsari da take son kwace dukkan kujerun gwamnonin kasar 36 zuwa APC.
Yayin martaninshi, Gwamna Abdullahi Sule ya yabawa Dakta Ganduje da kuma sauran wadanda suka sauya shekar zuwa jami'yyar APC mai mulkin kasar.
Sule ya kuma godewa Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume wurin tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaben da aka gudanar a farkon 2023.
Farfesa Anthony ya samu takarar Sanatan Ebonyi
A wani labarin, jami'yyar APC a jihar Ebonyi ta gudanar da zaben fidda gwani a mazabar Ebonyi ta Kudu a Majalisar Dattawa.
Farfesa Anthony Okorie shi ya samu nasarar lashe zaben da kuri'u 281 a cikin 285 da aka gudanar a yau Asabar.
Asali: Legit.ng