Zan Nuna Maka Ni Waye, Ministan Tinubu Ya Dira Kan Yaron Gidansa, Ya Gargade Shi Kan Zaben 2027
- Rikici ya kara dagule wa bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tura zazzafan gargadi ga yaron gidansa, Siminalayi Fubara
- Wike ya ce a yanzu ba lokacin siyasa ba ne amma idan lokacin ya zo za a gane waye ne a saman wani
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tura sakon gargadi ga Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Wike ya bayyana cewa a yanzu ba lokacin siyasa ba ne amma idan lokacin ya yi za a gane waye ne a sama.
Mene Wike ke cewa ga Fubara?
Ministan ya bayyana haka ne a yau Asabar 6 ga watan Disamba yayin ganawa da tsohon amininsa a siyasa, Cif Victor Giadom.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bai damu da dukkan zage-zagen da ake yi a kafofin yada labarai ba inda ya ce ba a zabe a kafar sadarwa, cewar Vanguard.
Ya kara da cewa lokacin zabe zuwa suka yi suka roki jama'a kuma suka amince dasu don haka ba a siyasa a kafafen sadarwa.
Wane gargadi Wike ya tura ga Fubara?
Ya ce:
"Yanzu ba lokacin siyasa ba ne, idan lokacin ya yi a nan za a gane waye a gaba.
"Idan kaga dama ka yi ta zagi na yadda kake so, ko ka dauko wasu a kafafen sadarwa su zage ni ban damu ba.
"Amma lokacin siyasa na zuwa, ba mu tsaya takara a kafafen sadarwa ba, mun yi wa mutane magana kuma sun amince da mu."
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike, cewar Channels TV.
An rushe Majalisar jihar Rivers
A wani labarin, Yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a jihar Rivers, Gwamna Siminalayi Fubara ya umarci rushe Majalisar jihar.
Wannan na zuwa ne yayin ake ci gaba da takun saka tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.
Daga bisani Shugaba Tinubu ya nuna rashin jin dadinsa kan rushe Majalisar inda ya ce ita ce martabar dimukradiyya.
Asali: Legit.ng