Ana Daf da Yanke Hukuncin Shari'ar Kano, Babban Lauya Ya Tura Sako Ga Sabbin Alkalan Kotun Koli 11

Ana Daf da Yanke Hukuncin Shari'ar Kano, Babban Lauya Ya Tura Sako Ga Sabbin Alkalan Kotun Koli 11

  • Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli musamman a Kano, babban lauya ya tura gargadi ga lauyoyin kotun
  • Lauya Yusuf Nuruddeen ya bayyana cewa an nada sabbin alkalan 11 a Kotun Koli a dai-dai lokacin da aka fi bukatarsu
  • Lauyan ya bayyana haka ne yayin hira da Legit inda ya ce kasancewar kasar ya dogara ne ga Kotun Koli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban lauya a Najeriya, Yusuf Nuruddeen ya shawarci sabbin alkalan Kotun Koli 11 kan adalci.

Nuruddeen wanda mazaunin jihar Legas ne ya ce an nada sabbin lauyoyin ne a lokacin da Najeriya ke bukatar adalci.

Kara karanta wannan

Kano: Babban Malami ya faɗi mafita 1 tak da ta rage wa Gwamna Abba gabanin hukuncin Kotun Koli

Babban lauya ya shawarci sabbin alkalai kan hukuncin shari'ar zabe
Babban Lauya Ya Tura Sako Ga Sabbin Alkalan Kotun Koli 11. Hoto: @nyt_optimist, @PO_GrassRootM.
Asali: Twitter

Mene lauyan ke cewa kan sabbin alkalan?

Yusuf ya ce a halin da ake ciki yanzu ne dai-dai lokacin tabbatar da adalci da bin doka a shari'ar da ake yi a kotunan zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya bayyana haka ne yayin hira da Legit inda ya ce kasancewar kasar ya dogara ne ga Kotun Koli.

Wannan sharhi nashi ya zo ne a lokacin da ake dakon shari'ar zaben gwamnan Kano wanda ke cike da kalubale ganin yadda shari'ar ta dauki hankulan 'yan kasar.

A kwanakin baya Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar inda ake sa ran daga yanzu komai na iya faruwa kan bayyana hukuncin karshe.

Wace shawara lauyan ya bayar?

Lauya ya ce akwai matsaloli a shari'ar da aka yi a baya musamman ta Sanata Ahmed Lawan da shari'ar Kano da sauran hukunce-hukuncen kotuna.

Kara karanta wannan

Shari'ar Kano: Mata sun yi gangami don nuna goyon baya ga Abba Gida-Gida gabanin hukuncin Kotun Koli

Ya ce:

"Ina ba su shawara su bi doka wurin yanke hukunci, bai kamata su saba wa mafi yawan 'yan kasa ba, sannan dole a yi adalci da ba da damar sauraran ko wane bangane."

Lauyan ya kara da cewa dole tun da akwai sabbin jini a cikinsu ya san za su tsaya wurin tabbatar da adalci, cewar Channels TV.

Kotu ta bai wa Abba Kabir wa'adin mako 1

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta bai wa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano wa'adin mako daya kan karar da aka shigar da shi.

Kotun ta umarci gwamnatin jihar Kano ta gurfana a gaban kotun a jiya Laraba 3 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel