Kano: Kotun Tarayya Ta Bai Wa Abba Kabir Wa'adin Mako 1 Kan Karar da Aka Shigar da Shi

Kano: Kotun Tarayya Ta Bai Wa Abba Kabir Wa'adin Mako 1 Kan Karar da Aka Shigar da Shi

  • A yau Laraba babbar kotun Tarayya ta bai wa gwamnatin jihar Kano wa'adin mako daya kan shari'ar da ake yi
  • Umarnin ya shafi karar da ciyamomin kananan hukumomi 44 da ke jihar kan kokarin taba kudaden asusunsu da gwamnan ke shirin yi
  • Kotun ta ba da wa'adin ne don gwamnatin jihar ta yi martani kan zarge-zargen da ake yi a kanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta bai wa gwamnatin jihar Kano wa'adin kwanaki bakwai kan karar da aka shigar da ita.

Ciyamomin kananan hukumomi 44 da kungiyar ALGON sun maka Gwamna Abba Kabir a kotun kan amfani da kudaden kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Rikita-rikita bayan gwamnan APC ya dakatar da ciyamomi 18 da kansiloli 33 a jiharsa, ya gargade su

Kotun Tarayya ta sake yin hukunci kan shari'ar Abba Kabir da ciyamomi
Kotu ta bai wa Abba Kabir wa'adin mako 1 kan karar da aka shigar da shi. Hoto: Abba Kabir.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kotun ta ba da wa'adin ne don gwamnatin jihar ta yi martani kan zarge-zargen da ake yi a kanta, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ya gabata kotun ta dakatar da hana gwamnan kan amfani ko kuma gudanar da kudaden asusun kananan hukumomin.

Sai dai gwamnatin jihar ba ta ce komai ba game da hukuncin kotun da ta gabatar a makon da ya gabata.

Martanin Alkalin kotun kan karar

Mai Shari'a, Donatus Okorowo shi ya ba da umarnin bayan lauyoyin ko wane bangare sun gabatar da bahasi kan shari'ar da ake yi.

A ranar Alhamis 28 ga watan Disamba, Okorowo ya dakatar da bukatar da ke neman hana Gwamna Abba Kabir taba kudaden kananan hukumomin.

A madadin haka, ya umarci wadanda ake karar su gurfana a gaban kotun a ranar 3 ga watan Janairu, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Bayan dan jarida ya yi fallasa, FG ta dakatar da ‘karbar’ digiri daga Togo da Jamhuriyar Benin

Ya bukaci gurfanar ta su ce don ba da dalili kan meyasa ba za a tabbatar da bukatar masu karar ba.

APC ta yi magana kan shari'ar jihar Kano

A wani labarin, jami'yyar APC mai mulkin Najeriya ta yi martani kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano.

Jam'iyya ta ce ta na da kwarin gwiwar samun nasara a shari'ar da ake yi tsakaninsu da NNPP.

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli bayan ta tanadi hukucin kan zaben jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel