Rikita-rikita Bayan Gwamnan APC Ya Dakatar da Ciyamomi 18 da Kansiloli 33 a Jiharsa, Ya Gargade Su

Rikita-rikita Bayan Gwamnan APC Ya Dakatar da Ciyamomi 18 da Kansiloli 33 a Jiharsa, Ya Gargade Su

  • Kwanaki kadan bayan hawa karagar mulki, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya dakatar da shugabannin kananan hukumomi
  • Bayan sallamar ciyamomin 18, gwamnan ya kuma dakatar da kansiloli guda 33 da ke wakiltar unguwannin jihar Ondo
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar kananan hukumomi da sa hannun Alonge Adewale ta fitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya dakatar da dukkan ciyamomin kananan hukumomi a jihar.

Bayan dakatar da ciyamomin guda 18, Lucky ya kuma sallami kansiloli guda 33 da ke wakiltar unguwannin jihar baki daya.

Gwamnan APC ya dakatar da ciyamomin 18 da kansiloli 33 a jiharsa
Gwamna Lucky ya dakatar da ciyamomin kananan hukumomi 18. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Yaushe gwamnan ya dakatar da ciyamomin?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar kananan hukumomi ta fitar da sa hannun Alonge Adewale, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Tarayya ta bai wa Abba Kabir wa'adin mako 1 kan karar da aka shigar da shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Mun samu labarin cewa wadanda aka dakatar daga kujerunsu su na ci gaba da kiran kansu a matsayin shugabanni.
"An umarce ni da in bukaci shugabannin gudanarwa a ma'iakatun da su karbi ragamar kananan hukumomi daga wadanda aka dakatar."

Wane hukunci kotun ta yanke?

Takardar ta kuma bukaci wadanda aka dakatar din su mika dukkan abin da ke hannunsu ga ma'aikatun da su ka wakilta.

Wannan mataki na zuwa ne bayan hukuncin kotu da Mai Shari'a, Yemi Fasanmi ya gabatar kan ciyamomin kananan hukumomin.

Hukuncin ya biyo bayan shigar da kara da jami'yyar adawa ta PDP ta yi kan dakatar da ciyamomin a jihar.

Wani daga cikin ciyamomin da aka dakatar da bai bayyana sunansa ya yi fatali da matakin na gwamnan jihar, cewar Daily Post.

Ya ce a baya sun sami wata sanarwa kan dakatar da hukuncin kotun a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan dan jarida ya yi fallasa, FG ta dakatar da ‘karbar’ digiri daga Togo da Jamhuriyar Benin

Gwamna Lucky ya Yi sabbin nade-nade

A wani labarin, gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya yi sabbin nade-naden mukamai a gwamnatinsa.

Lucky ya nada sakataren yada labaransa da kuma wasu mukamai guda uku bayan murabus din wasu daga cikin mukarraban gwamnatin.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a ranar Laraba 27 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.