Rikicin PDP: Jam'iyyar PDP Ta Yi Magana Kan Matsayin Kujerar Shugabanta da Aka Dakatar

Rikicin PDP: Jam'iyyar PDP Ta Yi Magana Kan Matsayin Kujerar Shugabanta da Aka Dakatar

  • Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya yi watsi da batun dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar Ondo, Fatai Adams
  • Kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce dakatarwar ta saɓawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ƙa’idojin jam’iyyar
  • Ologunagba ya bayyana matakin a matsayin cin zarafi kuma ya yi barazanar cewa kwamitin ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin ladabtarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na ƙasa (NWC) ya yi watsi da batun dakatar da Fatai Adams, shugaban jam’iyyar na jihar Ondo.

Kwamitin na NWC ya bayyana dakatarwar a matsayin wacce ba ta inganta ba domin ba ta yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba, cewar rahoton TVC News.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'o'in kasashen waje da gwamnatin Tinubu ta haramta a Najeriya

PDP ta yi watsi da dakatar da shugabanta na Ondo
Jam'iyyar PDP ta yi watsi da dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Ondo Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar a Abuja a daren ranar Talata, 2 ga watan Janairu, ya bayyana matakin a matsayin cin mutunci wanda za a yi hukunci a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce PDP jam’iyya ce mai tsari, kuma bin tsarin mulki da bin doka da oda ba zai bari dakatarwar ta cigaba da zama ba, rahoton Thisday ya tabbatar.

Ya ce hakan ya faru ne saboda ba za a bar wasu tsiraru ko ƙungiyoyi su karya kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Dalilin da yasa PDP NWC ta ƙi amincewa da dakatar da Fatai Adams

Ologunagba ya ce dakatarwar da aka yi wa shugaban na jihar Ondo haramun ne, wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulkin PDP.

Ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin ladabtarwa da ya dace domin kare zaman lafiya da tsarkin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi magana kan abu 1 da LP za ta kwace a hannun PDP

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Kwamitin NWC ya bayyana cewa Mista Fatai Adams shine shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Ondo, kuma ya buƙaci dukkanin shugabanni, masu ruwa da tsaki, mambobi da magoya bayan jam’iyyar mu a jihar Ondo da ƙasa baki ɗaya da su yi watsi da batun dakatarwar da aka yi.
"NWC ya buƙaci daukacin ƴaƴan jam’iyyar na Jihar Ondo da su cigaba da haɗa kan su kuma su cigaba da yin aiki tare domin kare muradun jam’iyyarmu da jama’a baki ɗaya."

Hadimin Atiku Ya Magantu Kan Sake Tsayawarsa Takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Daniel Bwala, hadimin Atiku Abubakar ya yi magana kan yiwuwar sake tsayawa takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasan a zaɓen 2027.

Bwala ya bayyana cewa Atiku Abubakar zai sake jaraba sa'arsa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng