"Akwai Matsala" Fitaccen Malamin Addini Ya Gano Makomar Gwamnan PDP Na Arewa a Kotun Koli

"Akwai Matsala" Fitaccen Malamin Addini Ya Gano Makomar Gwamnan PDP Na Arewa a Kotun Koli

  • Malami ya buƙaci Gwamna Celeb Mutfwang ya dage da addu'a ba don ya tsira da kujerarsa kaɗai ba harda neman kariya daga hare-hare
  • Joshua Iginla, wanda ya yi hasashen kan makomai gwamnan Filato a kotun koli, ya ce ya hangi wani mutum daban ya kwace kujerarsa
  • Gwamna Mutfwang da PDP sun tafi kotun koli domin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da ya ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya ci zaɓe a watan Maris

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, Jihar Plateau - Malamin addinin kirista na cocin Champions Royal Assembly, Joshua Iginla, ya yi hasashen makomar Gwamna Celeb Mutfwang na jihar Filato a kotun koli.

Idan baku manta ba Iginla shi ne ya jagoranci tawagar malamai a Najeriya, waɗanda suka yi hasashen nasarar Bola Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2023 tun kafin zaben.

Kara karanta wannan

Kano: Babban Malami ya faɗi mafita 1 tak da ta rage wa Gwamna Abba gabanin hukuncin Kotun Koli

Gwamnan Filato da Joshua Iginla.
Tsige Gwmanan Filato: Malami Ya Yi Hasashen Makomar APC da PDP a Kotun Koli Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Twitter

Meyasa kotun ɗaukaka ƙara ta tsige Mutfwang?

Yanzu haka dai Gwamna Mutfwang ya garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta tsige shi daga kujerar gwamnan jihar Filato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ɗaukaka ƙara ta tsige gwamnan Filato ne saboda rashin halastaccen tsari a jam'iyyar PDP ta jihar lokacin da ya tsaya takara a zaben 18 ga watan Maris.

Bayan haka ne kotun ta bayyana Nentawe Goshwe, ɗan takarar jam'iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Shin PDP zata kwato nasararta a kotun koli?

Da yake tsokaci kan makomar gwamnan a taron addu'o'in dare ranar 1 ga watan Janairu, 2023, Malamin ya roƙi Mutfwang ya dage da addu'a saboda ya hango matsala.

Joshua Iginla, ya bayyana cewa ya gani a wahayin da aka masa cewa Gwamna Mutfwang ya sauka daga madafun iko, wani daban ya karɓe mulkin jihar Filato.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dokokin jihar PDP ya yi murabus daga muƙaminsa, ya ajiye kujerar gaba ɗaya

Malamin addinin ya ci gaba da cewa gwamnan yana nufin jihar da alheri, amma ya gani a fili cewa wasu sheɗanu ba sa son ya karisa abin da ya fara.

A kalamansa ya ce:

“Ya kamata gwamna ya yi addu’a, na ga wani mutum ya karɓe kujerarsa, ya yi addu’a ya karasa abin da ya fara, gwamnan yana da niyya mai kyau, amma wasu a jihar Filato ba su so ya ci nasara."
"Ya kamata ya tashi tsaye ba wai domin kare kujerarsa kaɗai ba, har da ceton rayuwarsa. Tauraruwarsa na haskawa a ƙasar nan duk da abubuwan da suka dabaibaye shi."

Gwamnan Kano na cikin matsala a kotun ƙoli

A wani rahoton na daban Malamin addini ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dage da yin addu'a kan lafiyarsa gabanin hukuncin kotun kolin Najeriya.

Joshua Iginla, a hasashensa na abubuwan da zasu auku a 2024, ya ce ya hango kujerar Gwamna Yusuf na Kano tana tangal-tangal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262