Saura Kiris da Buhari Ya Nada Ni Mukami a 2015, In Ki Karbar Kujerar Inji Tsohon Minista

Saura Kiris da Buhari Ya Nada Ni Mukami a 2015, In Ki Karbar Kujerar Inji Tsohon Minista

  • Tsohon gwamnan na jihar Ekiti yake cewa ya sa ran zama ministan harkokin kasar waje ne a 2015
  • Sai ga shi ba hakan ta faru ba, shugaban kasa ya nada Kayode Fayemi ya rike ma’aikatar ma’adanai
  • ‘Dan siyasar ya ce kiris ya rage ya ajiyewa Muhammadu Buhari kujerarsa, amma a karshe ya hakura

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ekiti - John Kayode Fayemi ya ce kiris ya rage ya ki karbar mukamin minista da Muhammadu Buhari ya ba shi a shekarar 2015.

A wata hira da aka yi da shi a This Day, Dr. John Kayode Fayemi ya nuna bai taba tunanin zama ministan harkokon ma’adanai ba.

Buhari-Fayemi
Muhammadu Buhari ya ba Kayode Fayemi Minista Hoto: @yabaleftonline, @abati1990
Asali: Twitter

Minista: Kayode Fayemi ya so murabus

A cewarsa, ya yanke shawarar fadawa Muhammadu Buhari zai ajiye mukamin domin bai da masaniyar ofishin da aka ba shi.

Kara karanta wannan

A Jawabin Shiga 2024, Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ministoci da Hadiman da Zai Kora

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayode Fayemi ya ce a lokacin da Mai girma Buhari ya sanar da ministocinsa, shi bai san komai a kan harkar ma’adanai a kasar ba.

Jawabin Fayemi kan zama Minista

"Kafin zama ministan tarayya, ni ne darektan tsare-tsaren yakin zaben shugaban kasa, kuma na yi aiki da kwamitin karbar mulki
ina da cikakken haske a kan abubuwan da su ka faru a lokacin Jonathan, amma ban shirya zuwa ma’aikatar da aka tur ani ba
Da aka sanar da na zama ministan ma’adanan kasa, bari in fadi gaskiya, na yi mamaki.
Gaskiya nayi tunanin zama ministan waje ne, bangaren da na ke gaba wajen ba Buhari shawara gabanin zabe da nadin mukami."

- Dr. Kayode Fayemi

Ya aka yi Ministan ya hakura?

The Cable ta ce Niyi Adebayo da mai dakinsa su ka ba Fayemi shawarar ya hakura da batun kin karbar babban mukamin da aka ba shi.

Kara karanta wannan

2024: Abubuwa 10 da Tinubu ya fadawa Najeriya a jawabin shiga sabuwar shekara

Daga baya Buhari ya fadawa Fayemi da gan-gan ya aika shi ma’aikatar saboda ya ba noma, ayyuka da kuma ma’adanai muhimmanci.

A karshe Fayemi ya bar kujerar Minista

Kayode Fayemi wanda ya yi minista tsakanin 2015 – 2018 ya ajiye kujerar, ya sake neman takarar gwamnan Ekiti a karkashin APC.

Kafin ya bar ofis, jigon na APC ya shaida ya yi kokari wajen kawo cigaba a bangaren.

Abba Kabir Yusuf ya nada mukamai

A ranar Talata aka ji labari Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sakatarorin gwamnati da karin hadimai da za su rika taimaka masa a ofis.

Andrew Ma’aji wanda Fasto ne da Cif Chukwuma Innocent Ogbu sun samu shiga a matsayin masu taimakawa gwamnatin Abba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng