Fayemi ya lashe Zaben Fitar da 'Dan Takarar Gwamna na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

Fayemi ya lashe Zaben Fitar da 'Dan Takarar Gwamna na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

Kayode Fayemi, Ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari na ma'aikatar albarkatun kasa, ya lashe zaben fitar da dan takarar gwamna na jihar Ekiti a karkashin jam'iyyar APC.

Ministan wanda shine tsohon gwamnan jihar yayin da gwamna Ayodele Fayose ya ci galaba a kan sa a zaben 2015, ya riki nasarar hannun biyu-biyu a wannan karo yayin zaben fitar da dan takarar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Kayode Fayemi
Kayode Fayemi

Jaridar The Cable ta bayyana cewa, ministan ya lashe zaben ne da kuri'u 941 da ya sanya ya yiwa sauran 'yan takarar fintinkau na dukan kece raini.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi alkawarin daidaita tsarin Jami'o'in Najeriya

Kanwa uwar gami ta kula da wannan zabe, gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Tanko Al-Makura, ya bayar da tabbaci na adadin wakilai da suka kada kuri'un su yayin gudanar da wannan zabe.

Legit.ng ta fahimci cewa, duk da janye takarar sa tun cikin makon da ya gabata, babban hadimin shugaba Buhari, Babafemi Ojudu, ya samu kuri'u har goma yayin zaben fitar da dan takarar da aka gudanar a birnin Ado-Ekiti.

Ga jerin yadda sakamakon zaben ya kaya kamar haka:

Kayode Fayemi - 941

Segun Oni - 481

Kayode Ojo - 281

Olufemi Richard Bamisile - 179

Oluyede Oluwole - 121

Aluko Daniel Olugbenga - 86

Sesan Fatoba - 43

Bimbo Daramola - 28

Bamidele Faparusi - 23

Kola Alabi - 14

Yinka Akerele - 11

Babafemi Ojudu - 10

Kola Alabi - 8

Opoyemi Bamidele - 8

Aloba Adebisi - 7

Adesua Oladiran - 4

Adeyanju Bodunde - 3

Coker Olumuyiwa - 2

Olumilua Olumuyiwa - 2

Ajayi Olatunji - 2

Ayodele Arise - 2

Ajayi Adebowale Oluranti - 1

Oladipupo Ogunkoya - 1

Elizabeth Taiye - 1

Adekunle Patrick - 0

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel