Fitaccen Gwamnan APC Ya Kori Hadimansa Da Wasu Masu Rike Da Mukaman Siyasa

Fitaccen Gwamnan APC Ya Kori Hadimansa Da Wasu Masu Rike Da Mukaman Siyasa

  • Gwamnatin Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ta fara shirin mika mulki domin wa'adinsa ta kusa karewa
  • A yayin hakan, Gwamna Fayemi ya rushe wasu masu mukaman da ya nada a matsayin wani mataki na mika mulkin
  • Kazalika, shima Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi wan dan sauye-sauye a fadarsa

Ekiti, Ado - Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya sallami wasu daga cikin hadimansa da wasu masu rike da mukaman siyasa.

Gwamna Fayemi
Fitaccen Gwamnan APC Ya Kori Hadimansa Da Wasu Masu Rike Da Mukaman Siyasa. Hoto: Gwamna Kayode Fayemi.
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wadanda aka sallama cikin hadiman gwamnan sun hada da mashawarta na musamman, direkta janar, da shugabannin wasu hukumomin da ba karkashin minista suke ba da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

An sanar da hakan ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Mr Adejumo, sakataren dindindin na ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Kamar yadda jaridar Guardian ta rahoto, an sallami masu mukaman na Gwamna Fayemi ne don taimakawa wurin mika mulki ga sabuwar gwamnati.

An tattaro cewa sallamarsu zai taimaka kudadensu da allawus su fito da wuri a yayin da ake canjin gwamnatin.

Amma, an gano cewa wasu hukumomi da aka ambace su a sashi na 197 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima har yanzu suna bakin aiki.

A Oyo, Makinde ya sauya wa ma'aikata wurin aiki

Guardian ta rahoto cewa wani abu mai kama da wannan ya faru a jihar Oyo inda Gwamna Seyi Makinde ya sauya wa wasu yan fadarsa wurin aiki.

Kwamishinan labarai na jihar, Dakta Wasiu Olatubosun ya bayyana cewa Olasunkanmi Olaleye ne zai jagoranci Ma'aikatar Kananan Hukumomi da Sarautar Gargajiya yayin da Bayo Lawal zai jagoranci Ma'aikatan Cinikayya, Masana'antu, Saka Hannun Jari da Kungiyoyin Kasuwanci.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Yan Ta'adda 5 Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30

Laifin Tinubu Ne "Idan Amaechi Ya Koma PDP", Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

A wani rahoton, Chukwuemeka Eze, fitaccen jagora a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce a dora wa Bola Tinubu laifi idan Amaechi ya bar jam'iyyar.

Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yana zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.

Idan za a iya tunawa Eze a baya-bayan nan ya kasance yana magana kan Amaechi kuma ya ce idan Amaechi ya shiga PDP, laifin Tinubu ne, wato dan takarar shugaban kasa na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel