Atiku Ya Fadi Matsala 1 da Ta Wajaba Shugaba Tinubu Ya Shawo Kan ta a Shekarar 2024
- Atiku Abubakar ya fitar da jawabi na musamman a game da kashe-kashen da aka yi kwanan nan a Najeriya
- Wazirin Adamawa ya bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta magance matsalar tsaro da ake fama da ita
- Paul Ibe ya yi magana a madadin Atiku, ya ce dole a san yadda za a kama wadanda su ke kashe mutane
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Jagoran adawa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasar nan.
The Cable ta rahoto Atiku Abubakar yana mai cewa za a iya magance matsalar kashe-kashe idan har aka fadada tsare-tsaren tsaro.
An kashe mutane 190 a Filato
‘Dan takaran na jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya yi wannan magana ne ganin yadda aka hallaka mutane daf da kirismeti a jihar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hare-haren da aka kai a Bokkos, Barkin-Ladi, da Mangu sun jawo an rasa rayuka kusan 200.
2024: Jawabin Atiku Abubakar
A wani jawabi da ya fitar ta hannun Paul Ibe ranar Lahadi, Wazirin Adamawa ya bukaci a cafke duk wadanda su kayi wannan ta’adi.
Alhaji Atiku Abubakar ya ce bai kamata a kyale miyagu su yi barna ba tare da an cafke su ba, yin hakan ne kadai zai magance lamarin.
An rahoto ‘dan siyasar yana cewa mutane suna kiran jihohi su kafa ‘yan sandansu ne saboda irin gazawar jami’an tsaron da ake da su.
"Yadda aka samu matsala" - Atiku
A ra’ayin ‘dan adawar, Najeriya ta samu kan ta a wannan mawuyacin hali ne tun farko saboda yadda bangaren shari’a ya tabarbare.
Atiku yake cewa kotu tana sakin masu laifi ba tare da an yi shari’ar gaskiya ba, wanda hakan ya na karya kwarin gwiwar jami’an tsaro.
A karshen jawabin da ya fito daga Paul Ibe, Atiku yace ya so ya ziyarci garuruwan da aka kai hari, sai dai kuma ba ya nan a halin yanzu.
Tsohon mutumin Atiku ya samu mukami
Ku na da labari da aka tashi rabon Darektoci, Festus Keyamo ya tuna da mai taimakawa tsohon mataimakin shugaban Najeriya.
Micheal Achimugu wanda ya yi aiki da Atiku Abubakar da ‘yan gidansa ya zama Darektan sadarwa a hukumar nan ta NCAA a yanzu.
Asali: Legit.ng