Jam’iyyar PDP Ta Ba Ma’aikatan Najeriya Su Tuburewa Gwamnatin Tinubu Kan Muhimmin Lamari

Jam’iyyar PDP Ta Ba Ma’aikatan Najeriya Su Tuburewa Gwamnatin Tinubu Kan Muhimmin Lamari

  • Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana shawarinta ga ma’aikatan Najeriya a ranar da ake bikin ranar ma’aikata
  • Ta ce ya kamata ma’aikata su tsaya tsayin daka wajen tuburewa gwamnatin APC da ke barazana ga dimokradiyya
  • Akwai tsama tsakanin jam’iyyar adawa ta PDP da APC mai mulkin kasa da ta shafe shekaru takwas na mulki

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta bukaci ma’aikatan Najeriya da su kara kaimi wajen tunkarar masu cin dunduniyar dimokradiyya da ke neman yin kememe ga mulkin kasar nan, rahoton Leadership.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ne ya bayyana haka a lokacin da yake jinjina wa ma’aikatan Najeriya a bikin ranar ma’aikata ta bana tare da takwarorinsu na duniya.

Ologunagba ya ce PDP na yabawa ma’aikatan Najeriya bisa jajircewarsu da aminci da kishin kasa wajen yi wa kasarsu hidima duk da wulakanci da matsin da suke fuskanta.

Kara karanta wannan

"Ya mayar da Najeriya sansanin gudun hijira": PDP ta caccaki Tinubu kan muhimmin abu 1

PDP ta ba ma'aikatan Najeriya shawari
PDP ta ce ma'aikatan Najeriya su tuburewa gwamnatin APC | Hoto: Muhammad Adamu, Peoples' Democractic Party
Asali: Facebook

Dalilin wahalhalun ‘yan Najeriya

Ya kuma ta’allaka walhalun ma’aikatan da manufofin tattalin arzikin masu tsauri na jam’iyyar APC da aka shafe shekaru takwas ana fama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Gangancin tauye hakki, jin dadin rayuwa da damar ma’aikatan Najeriya na nuna gaskiyar mun rashin mutunci, rashin tausayi da rashin kula na gwamnatin APC da ke sha’awar cutar da ‘yan kasa.”

Ma’aikatan Najeriya na cikin tashin hankali

Ya kara da cewa, da yawa daga cikin ‘yan Najeriya musamman ma’aikata na cikin bakin ciki dangane da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, TheCable ta ruwaito.

A bayanansa, sakamakon zaben 2023 na kunshe da cin zarafi da magudi da murdiya da sauya sahihin sakamako da kuma zagon kasa ga burin jama’a.

Jam’iyyar ta bukaci ma’aikatan Najeriya da su yi amfani da karfi da ikonsu a kasar wajen kare turbar dimokuradiyya daga masu amfani da siyasadon cimma son ransu.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Minista ta ba ‘yan Najeriya kwarin gwiwa

A gefe guda, ministar jin kai ta Najeriya, Betta Edu ta karfafa gwiwar 'yan kasar, inda tace talakawa su kwantar da hankali abubuwa za su daidaita a sabuwar shekara.

Ta bayyana hakan ne a cikin sakon da ta fitar na taya 'yan kasa murnar shiga sabuwar shekarar 2024 mai kamawa nan da sa'o'i kadan, rahoton Vanguard.

Ta bayyana cewa, gwamnatin shugaba Tinubu ta kawo shirye-shirye da dama da za su fitar talakawa daga halin kaka-ni-kayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.