Ba a Gama da Kame ’Yan Badala Ba, Hisbah Ta Juyo Kan Mabarata a Jihar Katsina

Ba a Gama da Kame ’Yan Badala Ba, Hisbah Ta Juyo Kan Mabarata a Jihar Katsina

  • Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta ce ba za ta lamunci ci gaba da ganin mabarata a jihar ba, ta bayyana matakin da za ta dauka
  • Rahoto y ace, za a tantance tare da daukar matakin rage yawaitar barace-barace a kan titunan jihar da ke Arewa maso Yamma
  • Arewacin Najeriya na daga bangaren da ke fama da yawaitar mabarata a kan tituna, gwamnati na ci gaba da hango hanyoyin magance hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Katsina - Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta jaddada kudirinta na daukar mataki kan yawaitar barace-barace a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.

Dr Aminu Usman (Abu-Ammar), babban kwamandan hukumar Hisbah a Katsina ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Asabar.

A cewarsa, gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa don tsaftace jihar daga duk wani nau’in lalata da barnar da ka iya biyo baya, Pulse ta tattaro.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 100 a filato, majalisa ta nemi zama da jigogin tsaro

Za a hana bara a jihar Katsina
Yadda Katsina za ta hana bara a titunan jihar | Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Abin da Hisbah tasa a gaba

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwamnatin jihar tana kokarin hana barace-barace a fadin jihar saboda baya cikin addininmu.
“Bara na bata sunan addininmu da al’ummarmu ne kawai.
“Dokar da ta kafa hukumar Hisbah ta ba mu damar duba ga duk wani lungu da sako na jihar, don nemo mabarata a tituna da kuma tantance su.
"Za mu duba su ne don gano wadanda ke da matukar bukatar taimako sannan mu mika su ga hukumar Zakka da Wakafi domin nema musu taimako."

Matsayar gwamnatin Katsina

Ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Dikko Radda ne ya kafa hukumar Zakka da Wakafi don tallafa wa masu bukatar taimako, People Gazette ta tattaro.

Sai dai, Abu-Ammar ya bayyana cewa bayan an tantance wadanda suka fito daga wasu jihohi, za a mayar da su jihohinsu tare da mika su ga hukumomin da suka dace a can.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe yan sanda, sun sace fasinjojin da suka tafi hutun Kirsimeti

Ya ja hankalin iyaye da sauran al’ummar jihar, da su rika sanya ido a kan ‘ya’yansu, domin gwamnati ba za ta kara lamuntar hali irin wannan ba.

An nada sabon shugaban Hisbah a Katsina

A tun farko, Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya nada Ahmad Daku a matsayin shugaban Hukumar Hisbah a jihar.

Daku shi ne tsohon gwamnan jihohin Kano da Sokoto a mulkin soja kafin ya yi ritaya daga aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel