"Ya Mayar da Najeriya Sansanin Gudun Hijira": PDP Ta Caccaki Tinubu Kan Muhimmin Abu 1

"Ya Mayar da Najeriya Sansanin Gudun Hijira": PDP Ta Caccaki Tinubu Kan Muhimmin Abu 1

  • Ana zargin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mayar da ƙasar nan wani ƙaton sansanin ƴan gudun hijira (IDP)
  • Jam’iyyar PDP ta ce gazawar da gwamnatin Tinubu ta yi wajen biyan ma’aikata albashin watan Disamba ya tabbatar da shirinsa na takaici da cutar da ƴan Najeriya
  • Sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya ce ya kamata gwamnatin APC ta biya ma’aikata albashin watan Disamba sannan ta biya su diyya da aƙalla kaso 50%

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan rashin biyan albashin ma’aikata a watan Disamba domin murnar bukukuwan ƙarshen shekara.

Babbar jam’iyyar adawar ta ce gwamnatin Tinubu ta mayar da ƴan Najeriya mabarata, sannan kuma ƙasar ta zama sansanin ƴan gudun hijira na cikin gida.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

PDP ta caccaki Shugaba Tinubu
Rashin biyan albashin watan Disamba ya sanya PDP ta caccaki Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba ta shafin jam'iyyar na X @OfficialPDPNig.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ologunagba ya ce gazawar da gwamnatin Tinubu ta yi na biyan albashin watan Disamba ya tabbatar da cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shirya tsaf domin fusata ƴan Najeriya da ƙara musu raɗaɗi.

PDP ta caccaki gwamnatin Tinubu

Ya ce rashin biyan albashi wata hanya ce da gwamnatin APC ta ke amfani da ita wajen ɗaukar nauyin talauci da murƙushe jama’a don miƙa wuya ga mulkin kama-karya.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Irin wannan rashin zuciya da gwamnatin APC mara kishin jama'a ta nuna bai taɓa faruwa ba a cikin shekaru 16 da PDP ta yi tana mulki inda ma’aikata suka karɓi albashin watan Disamba kafin ranar Kirsimeti (25) don ba su damar yin bukukuwan ƙarshen shekara tare da masoyan su."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nuna alhini kan rasuwar Ghali Na'Abba, ya aike da sako mai muhimmanci

PDP ta buƙaci gwamnatin Tinubu da ta biya ma’aikata albashin watan Disamba tare da biyan su diyyar aƙalla kaso 50% na albashin su domin rage wahalhalun da ake ciki a ƙasa.

"PDP na buƙatar a gaggauta biyan albashin ma’aikata a watan Disamba tare da ƙara biyan diyyar aƙalla kaso 50% na albashin ma’aikata domin rage wahalhalun da gwamnatin APC ta ƙaƙaba musu." A cewarsa.

PDP Ta Shawarci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shawarci Shugaba Tinubu kan harin Plateau.

Jam'iyyar ta buƙaci shugaban ƙasar da ya ziyarci jihar Plateau da kansa domin jajanntawa waɗanda harin ya shafa, maimakon ya riƙa tura wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel