Abin da Ya Sa Mu Ka Kara Naira Tiriliyan 1.2 a Kasafin da Tinubu Ya Gabatar Inji Majalisa

Abin da Ya Sa Mu Ka Kara Naira Tiriliyan 1.2 a Kasafin da Tinubu Ya Gabatar Inji Majalisa

  • Abubakar Kabir Abubakar ya yi bayanin abin da su ka hango wajen yin kari a kundin kasafin kudin 2024
  • Shugaban kwamitin kasafin na majalisar wakilan tarayya ya ce tashin farashin kaya ya shafi kudin ayyuka
  • Hon. Abubakar ya ce kudin shigan kamfanonin gwamnati zai karu kuma an canza farashin Dala a kasafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban kwamitin kasafi a majalisar tarayya, Abubakar Kabir Abubakar ya yi magana a kan karin da aka yi a kasafin kudi.

Premium Times ta rahoto Abubakar Kabir Abubakar (APC, Kano) yana cewa an yi karin ne saboda hauhawar farashin kaya a Najeriya.

Kasafin kudi
Kasafin kudin 2024 a Majalisa Hoto: Kashim Shettima, House of Representatives
Asali: Facebook

Abubakar Kabir Abubakar ya ce sannan kamfanonin gwamnati da aka fi sani da GOE sun yi alkawarin samun karin N700bn a kudin shiga.

Kara karanta wannan

Kasafin 2024: Ana rashin kudi, ‘yan majalisa sun kara Naira Biliyan 147 a kasonsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasafin kudi: Dalilan da majalisar tarayya ta bada

‘Dan majalisar wakilan ya bayyana haka ne da yake jawabi wajen amincewa da kasafin na 2024 a zama na musamman da aka yi jiya.

Saboda a kammala aikin kasafin kudin, ‘yan majalisar tarayya sun yi aiki ranar Asabar.

Jawabin shugaban kwamitin kasafin kudi

"Muna da matsalar tashin farashi da canjin Naira a kan Dala, bangaren zartarwa sun kawo shawarar canjin N750 a kan Dala,
Bayan mun yi nazari da kyau, mun duba, hakan ba zai yiwu ba.
Saboda haka mun kara shi zuwa N800. Kuma bayan zama da GOE, sun yarda cewa za su kara kudin shigar da za su tatso.
A haka mu ka iya kara N1.2tr wanda ya shafi kudin yin ayyuka."

- Abubakar Kabir Abubakar

Za a ji dadin kasafin kudin 2024

Kara karanta wannan

Bayan shafe shekaru 7 a kulle, an sake bude masallacin Juma'a da gwamnan PDP ya shiga lamarin

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto, wannan karo kudin ayyukan more rayuwa sun zarce kudin kashewar yau da kullum a kasar.

Baya ga haka, Abubakar Kabir Abubakar ya ce an ware N850bn a kan harkar ilmi, ya kara da cewa al’umma za su ji dadin kasafin kudin na 2024.

Karin kudin majalisa a kasafi

‘Yan majalisar kasar sun kara kasafinsu zuwa N344.48b wanda shi ne mafi girma a tarihi kamar yadda aka samu labari a karshen makon nan.

An gano cewa 'yan majalisar tarayya sun yi karin N147bn a lissafin kasafinsu na N197bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng