Rikicin PDP: Gwamna Adeleke Ya Gana da Fayose, Ya Bayyana Sabon Lissafinsu
- Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya gana da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a gidansa da ke Legas
- Adeleke ya bayyana cewa an dauki matakin ne don warware rikicin da ya dabaibaye PDP a Kudu maso Yamma
- A cewar gwamnan, akwai bukatar hada kan shugabannin PDP na baya da na yanzu domin daidaita jam'iyyar a matakin kasa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Osogbo, Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya gana da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a kokarinsa na magance rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a kudu maso yamma.
A wata da ya yi a ranar Asabar, gwamnan na Osun ya bayyana cewa ya fara tuntuba domin magance rikicin da ya dabaibaye jam'iyar a yankin, wanda hakan ne yasa shi ziyartar gidan tsohon gwamnan a Legas.
A cewar Adeleke, hadin kai tsakanin shugabannin PDP na da da na yanzu a yankin kudu maso yamma na da matukar muhimmanci wajen daidaita jam'iyyar adawar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rikicin PDP ya fara a kudu maso yamma
Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar PDP a yankin kudu maso yammacin kasar ta raba gari da shugabancin jam'iyyar na kasa.
Mafi yawancin shugabannin yankin sun nuna adawa kan dan takarar shugaban kasa da shugaban jam'iyyar na kasa su fito daga arewa, amma sam PDP ta kasa ta yi kunnen uwar shegu da batun.
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben da tsohon shugaban jam'iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, sun bayyana cewa za a sauya tsarin shugabancin jam'iyyar bayan zaben.
Wannan matakin na daya daga cikin abubuwan da suka sa PDP ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023 inda APC mai mulki ta yi nasara.
Amma Gwamna Adeleke ya ce yana kan hanyar hada kan PDP. Ya ce:
“Mun tattauna kan muhimmancin hadin kai a tsakanin shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar mu a yankin Kudu maso Yamma, na da da na yanzu, Mista Ayodele Fayose (@GovAyoFayose), matakin daidaita jam’iyyar a matakin kasa."
Ga wallafar a kasa:
Adeleke ya magantu kan kujerar Shugaban kasa
A wani labarin, mun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana aniyarsa ta kwadayin neman shugabancin Najeriya.
Adeleke ya ce ya tabbatar ya cancanci kujerar shugabancin kasar inda ya ce da zarar ya samu dama ba zai bar ta ba.
Asali: Legit.ng