Kotu Ta Hana PDP Kwace Kujerar 'Yan Majalisar Rivers 27 da Suka Sauya Sheka Zuwa APC
- Minista Nyesom Wike ya yi nasara bayan kotu ta yi hukunci kan shari'ar 'yan Majalisun jihar Rivers guda 27 da suka sauya sheka
- Yayin hukuncin, kotun ta tsawaita dakatar da hukumar INEC da PDP kan korar 'yan Majalisar daga kujerunsu
- Hukuncin na zuwa ne bayan 'yan Majalisun jihar 27 sun sauya sheka zuwa APC daga jami'yyar PDP mai mulkin jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan shari'ar 'yan Majalisun jihar Rivers 27.
Kotun ta tsawaita dakatar da hukumar INEC da PDP kan korar 'yan Majalisar daga kujerunsu.
Wane hukunci kotun ta yanke kan shari'ar?
Har ila yau, kotun ta dakatar da hukumar ta INEC kan gudanar da zabe don maye gurbin wadanda suka sauya sheka, kamar yadda The Nation ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan 'yan Majalisun jihar 27 sun sauya sheka zuwa APC daga jami'yyar PDP mai mulkin jihar.
Mai Shari'a, Donatus Okorowo ya tsawaita dakatarwar a jiya Alhamis 28 ga watan Disamba bayan karar da lauyan mambobin Majalisar, Steve Adehi ya shigar.
Mene martanin Alkalin kotun kan shari'ar da ake yi?
Lauyan Majalisar jihar, Ken Njemanze bai yi korafi kan wannan hukunci da alkalin kotun ya yanke ba, cewar gidan talabijin na Channels.
Har ila yau, Mai Shari'a, Okorowo ya yi fatali da korafin lauyan PDP, Adeyemi Ajibade tare da amincewa da na Adehi.
'Yan Majalisar da suka sauya sheka na goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Bayan sauya shekar 'yan Majalisun, Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin shekarar 2024 a gaban mambobin Majalisar guda hudu kacal a gidan gwamnati.
An rushe Majalisar jihar Rivers
A wani labarin, Gwamna Siminalayi Fubara ya umarci rushe Majalisar jihar Rivers don yin kwaskwarima.
Gwamnan ya bayyana dalilin rushe Majalisar inda ya ce babu wata alakar siyasa kan maganar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin gwamnan da mai gidansa, Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng