Kotun Koli: Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke Kan Shari'ar Gwamnan APC da Dan Takarar PDP
- Taƙaddamar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa na cigaba da tayar da ƙura a tsakanin al'ummar jihar
- Wasu ƙungiyoyin mata da ba su gamsu da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba na cigaba da gudanar da zanga-zanga a jihar
- Ƙungiyoyin sun koka kan rashin adalcin da suka ce an yi musu, inda suka kai kukansu a gaban kotun ƙoli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Wasu mata a jihar Nasarawa sun sake gudanar da zanga-zanga a garin Lafia babban birnin jihar a ranar Talata.
Matan sun gudanar da zanga-zangar ne kan abin da suka bayyana a matsayin rashin adalcin da aka yi wa ɗan takarar gwamnan jihar, David Ombugadu, na jam’iyyar PDP, cewar rahoton The Punch.
A ranar 2 ga watan Oktoba ne kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta kori Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC, tare da bayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rashin gamsuwa da hukuncin, Sule ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara inda aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Menene buƙatun masu zanga-zangar?
Da take magana da manema labarai a Lafia a ranar Talata, shugabar ƙungiyoyin mata masu zanga-zangar, Hanatu John, ta ce dimokuradiyya ta shafi ƙuri’un jama’a ne.
Hanatu ta yi mamakin dalilin ƙin bayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.
A kalamanta:
"Mun fara zanga-zangar ta wannan makon ne a ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, saboda bikin Kirsimati ya zama mara armashi tunda an yi mana ƙwacen nasara."
"Mun kasance a nan tun watan Maris muna nuna rashin amincewa da abin da muka bayyana a matsayin rashin adalci na zaɓe. A lokacin zaɓen gwamna mun zaɓi Ombugadu ba Sule ba. Amma muna fatan za a yi abin da ya dace a kotun ƙoli."
"Domin haka muna kira ga alƙalai da su duba sakamakon zaɓen gwamna da aka yi daga jihar Nasarawa cikin natsuwa domin a dawo mana da nasarar mu."
Gwamna Sule Ya Zargi PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya zargi jam'iyyar PDP da shirin tayar da zaune tsaye a jihar.
Gwamnan ya yi nuni da cewa jam'iyyar na son yin amfani da bambance-bambancen addini da ƙabila domin kawo hargitsi a jihar.
Asali: Legit.ng