Labari da Dumi-Dumi: Tsohon Shugaban Majalisa, Ghali Na’Abba Ya Bar Duniya

Labari da Dumi-Dumi: Tsohon Shugaban Majalisa, Ghali Na’Abba Ya Bar Duniya

  • Rt. Ghali Umar Na’Abba ya rasu a makon nan yana mai shekara 68 da haihuwa a duniya
  • Babban ‘dan siyasar ya rike shugaban majalisa da Rt. Hon. Imam Salisu Buhari ya yi murabus
  • Marigayi Ghali Umar Na’Abba ya yi tashe ne a lokacin da Olusegun Obasanjo yake mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Ghali Umar Na’Abba ya rasu.

Da safiyar Laraba, 27 ga watan Disamba 2023, Leadership ta fitar da rahoto cewa Rt. Ghali Umar Na’Abba ya cika.

Ghali Umar Na’Abba
Ghali Umar Na’Abba ya rasu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ya aka yi Ghali Umar Na’Abba ya rasu?

Bayanai sun nuna fitaccen ‘dan siyasar ya bar duniya ne yana mai shekara 68 da haihuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisan Tarayya da Dokoki da suka mutu a shekarar 2023 kwanaki da cin zabe

Har zuwa yanzu da mu ke hada rahoton, ba a samu cikakken bayani game da mutuwar Ghali Na’Abba ba.

Daily Nigerian ta ce Marigayin ya rasu ne a safiyar yau watau Laraba a wani gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wata majiya ta shaida cewa Na’Abba ya yi fama da ‘yar rashin lafiya kafin rasuwarsa.

Takaitaccen tarihi Ghali Umar Na’Abba

Legit ta fahimci an haifi tsohon ‘dan majalisar tarayyar ne a unguwar Tudun Wada a birnin Kano cikin shekarar 1958.

Bayan ya yi firamare a Jakara da Rumfa College tsakanin 1969 zuwa 1974, ya tafi makarantar sharar fage a Kano.

A shekarar 1976 Na’Abba ya shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya samu digirin harkar siyasa a Oktoban 1979.

Siyasar Ghali Umar Na’Abba

Marigayin yana cikin daliban Marigayi Malam Aminu Kano a siyasa, tun yana karatun jami’a ya shiga gwagwarmayar PRP.

A shekarar 1999 ne Ghali Na’Abba ya zama ‘dan majalisar wakilan tarayya har ta kai ya jagoranci ‘yan majalisar kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya sun dira Legas, sun shiga ganawa da Shugaba Tinubu

Na'Abba ya zama Shugaban majalisa

Da aka samu Imam Salisu Buhari da badakalar takardar karatu, dole ‘dan majalisar ya sauka daga kan kujerarsa a 1999.

Na’Abba ya nemi tazarce a zaben 2003 amma shi da jam’iyyarsa ta PDP duk ba su yi nasara a jihar Kano a lokacin ba.

Tun da Na’Abba ya fadi zaben 2003 a hannun ANPP, bai sake rike wani babban mukami ba har ya yi ta sauya-sheka.

An rasa rayuka a jihar Kaduna

Kun ji labarin gudumuwar da mutane su ka bada bayan harin da aka kai wa ‘yan Maulidi a Tudun Biri a Kaduna.

Mutanen Tudun Biri sun samu taimakon fiye da N500m daga wajen Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilan tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng