Allah ya yi wa babban jigon Kano, Salisu Buhari rasuwa yana da shekara 83
A ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu ne aka binne gawar mahaifin tsohon kakakin majalisar tarayya, Alhaji Salisu Buhari a Kano.
Marigayi shahararren dan kasuwan ya rasu a asibitin kasar Masar a ranar Litinin yana da shekara 83 bayan yayi jinyar rashin lafiya.
Gawarsa da aka dauko daga kasar Masar, ya iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a yammacin ranar Laraba, inda yan uwa da abokam arziki suka tarbe shi.
Daga ccikin manyan mutanen da suka tarbi gawarsa a filin jirgin sasa sun hada da, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, mataimakinsa, Alhaji Nasiru Gawuna, mambobin majalisar dokokin jihar da kuma yan kasuwa.
Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II, ne ya jagoranci sallatar gawar tare da babban limamin babban masallacin Juma’a na Kano, Farfesa Sani Zahradeen, Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, mambobin masarautar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje da mataimakinsa, Gawuna.
KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Kungiyar matasan arewa ta mara wa Ahmed Lawan baya
Sauran sun hada da Alhaji Aminu Dantata, dan uwan marigayin Alhaji Sani Buhari, dan marigayin Ibrahim Salisu Buhari da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da sauransu.
An binne marigayin ne a makabartar ahlinsa da misalin karfe 5:30 na yamma a Goron Dutse da ke karamar hukumar Gwale a birnin Kano.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng