Kano da Jihohin da Ganduje Ya Ke Niyyar Karbowa APC Daga Hannun Jam’iyyun Adawa

Kano da Jihohin da Ganduje Ya Ke Niyyar Karbowa APC Daga Hannun Jam’iyyun Adawa

  • Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje tana yunkurin kara shiga jihohin jam’iyun adawa
  • APC mai mulki ta kama hanyar karbe karin jihohi a kotun zabe bayan PDP da NNPP sun fara gyara zama a mulki
  • Mahaifar sabon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ta Kano tana cikin jihohin da jam’iyya mai-ci take hari a yau

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rahoton nan ya tattaro wasu jihohin da ake tunanin za su iya fadawa hannun jam’iyyar APC nan ba da dadewa ba.

1. Kano

Kwanakin bayan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dauki alwashi APC za ta karbe mulki daga hannun Abba Kabir Yusuf.

Dr. Abdullahi Ganduje ya ce jam'iyyar NNPP ta lashe zabe ne ba tare da halataccen ‘dan takara ba, kuma an sabawa ka’idojin zabe na kasa.

Kara karanta wannan

Kaddara ta riga fata: Jerin 'yan takara 9 da suka mutu daf da shirye-shiryen zabe a 2023

Shugaban APC
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje Hoto: @OfficialAPCNg, @SimFubaraKSC, @Kyusufabba
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Filato

Jam’iyyar APC ta samu nasara a kotun daukaka kara a shari’ar zaben gwamnan Filato, idan ta samu yadda ta ke so za a tsige gwamnatin PDP.

Lauyoyin Nentanwe Yilwatda sun yi ikirarin PDP ta shiga zaben 2023 ne ba tare da tsaida shugabannin da ke da hakkin fito da ‘yan takara ba.

3. Anambra

Rahoton Daily Trust ya nuna Abdullahi Ganduje ya jawo Ifeanyi Ubah cikin APC ne a kokarin ganin an kifar da mulkin APGA a jihar Anambra.

An yi shekara da shekaru jam’iyyar APGA ta na rike da Anambra. Ganduje da ‘yan majalisarsa za su so APC ta doke Charles Soludo a 2026.

4. Ribas

Rahotanni sun ce Abdullahi Ganduje ya sauke shugabannin jam’iyyar APC ne saboda ya karfafawa Nyesom Wike daga yanzu zuwa zabe mai zuwa.

Wike ya tabbatar da ba zai tsaya takara da Bola Tinubu a 2027, yunkurin da NWC ta ke yi zai iya ba Ministan dama wajen rusa jam’iyyar PDP a Ribas.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban APC ya haddasa fitina, ya fadi yadda aka kashe N800m saboda a doke PDP

5. Zamfara

Abin da APC za ta so shi ne kotun koli ta tsige PDP ko a tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara da nufin Bello Matawalle ya koma kan mulki.

Gwamna Dauda Lawal ya karbe APC mai mulki daga hannun jihar a karon farko a zabe.

APC za ta so ta karbe Osun

Kamar a Ribas, nan gaba APC za ta yi bakin kokarinta wajen ganin jihar Osun ta koma hannunta bayan nasarar da ya yi mata ciwo a kotun koli.

Gwamna Ademola Adeleke ya taimaki Atiku Abubakar sosai a zaben 2023, Bola Tinubu da Ministansa, Gboyega Oyetola ba su so haka a 2027 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng