Za Mu Shawo Kan Dukkan Matsaloli Tare da Karfafa Najeriya - Ganduje

Za Mu Shawo Kan Dukkan Matsaloli Tare da Karfafa Najeriya - Ganduje

  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya aika sako karafafa gwiwa ga yan Najeriya gabannin shiga sabuwar shekara
  • Ganduje ya nuna kwarin gwiwar cewa gwamnatin da jam'iyyarsa ke jagoranta za ta shawo kan dukkan kalubalen da kasar ke fuskanta
  • Tsohon gwamnan na Kano ya kuma yi kira ga hada hannu wajen gina Najeriya tare da karfafa ta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin jam’iyyarsa za ta shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta, kuma cewa yan Najeriya za su hada hannu wajen gina kasa mai karfi da wadata.

Ganduje ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki na bikin Kirsimeti a ranar Litinin, 25 ga watan Disamba dauke da sa hannun sakataren labaran, Edwin Olufu, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje

Ganduje ya yi wa Najeriya fatan alhairi yayin bikin kirsimeti
Za Mu Shawo Kan Dukkan Matsaloli Tare da Karfafa Najeriya - Ganduje Hoto: OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

Ganduje ya yi kira ga karfafa Najeriya

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kuma ce lokaci ya yi da za a tuna da soyayya da albarkar haihuwar Yesu da aka yi wa kiristoci da kuma rungumar kyawawan dabi’u wanda ke cike da fata nagari, sadaukarwa, zaman lafiya, da farin ciki, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Najeriya na da dimbin albarkatu, kuma mun yi imani da cewa tare da kokari da sadaukar da kai, za mu iya shawo kan dukkan kalubalen da ke gabanmu.
“Yayin da muke bikin Kirsimeti, sai mu tuna da karfin hadin kai, kauna, da sadaukarwa. Mu yi shirin shiga sabuwar shekara, dauke da sabbin fata, azama da jajircewa wajen gina Najeriya da za mu yi alfahari da ita.
“Babbar addu’ata ita ce cewa wannan lokacin bukukuwan ya kusantar da mu ga mafarki da burinmu, sannan Allah ya sa shekara mai zuwa ta zama shaida ga kudurinmu na gina Najeriya mai karfi da wadata.

Kara karanta wannan

Akwai haske a 2024: Tinubu ya yi gagarumin alkawari gabannin shiga sabuwar shekara, ya fadi dalili

"Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin na alheri don dinke baraka, gyara dangantaka, da yada aminci a tsakanin al'ummominmu."

Kukah ya yi kira ga Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa Fitaccen Fasto a Najeriya, Mathew Hassan Kukah ya gargadi Shugaba Tinubu kan irin mulkin da ya ke yi a kasar.

Kukah ya ce Ubangiji da sauran 'yan Najeriya ba za su yafe wa shugaban ba idan har bai kawo sauyi a kasar ba.

Faston ya bayyana haka ne yayin jawabin bikin Kirsimeti a yau Litinin 25 ga watan Disamba a Sokoto, cewar Premium Times.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng