Shari'ar Zaben Kano: Kwankwaso Ya Jagoranci Addu'o'in Samun Nasarar Abba Kabir, Bayanai Sun Fito
- Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya jagoranci addu'a ta musamman a gidansa
- Kungiyar Mu'assatul Kwankwasiyya ita ta kirkiri addu'a karkashin jagorancin Mallam Yahaya Sufi
- An shirya addu'ar ce don samun nasara a shari'ar da akee yi ta zaben gwamnan jihar da ke Kotun Koli
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jagoran siyasar jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya jagoranci addu'a ta musamman a gidansa da ke jihar.
Wannan addu'a an shirya ta ne don samun nasara a shari'ar da ke yi ta zaben gwamnan jihar da ke Kotun Koli.
Mene dalilin yin addu'ar a Kano?
Kungiyar Musulunci ta Mu'assatul Kwankwasiyya ita ta kirkiri addu'a karkashin jagorancin Mallam Yahaya Sufi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran jagororin sun hada da Mallam Ashiru Nata'ala da Mallam Sadiq Rabi'u da kuma Bazallahi Nasiru Kabara, cewar Daily Trust.
Yayin da suke addu'ar, malaman sun yi addu'ar samun nasara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a Kotun Koli.
Taron addu'ar ya samu halartar manyan masu mukamai a gwamnatin Abba da kuma magoya bayan Sanata Kwankwaso.
Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?
A ranar Alhamis 21 ga watan Disamba Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano, cewar The Nation.
Tun farko, Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben Gwamna Abba Kabir saboda rashin kasancewarsa dan jam'iyyar NNPP.
Kafin hukuncin Kotun Daukaka Kara, kotun zabe a jihar ita ma ta tsige gwamnan saboda dalilan kara masa kuri'u wadanda ba su inganta ba.
Kwankwaso ya ziyarci Tudun Biri a Kaduna
A wani labarin, Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara kauyen Tudun Biri don jajantawa mutanen kauyen kan iftila'in da ya auku.
Kwankwaso ya bukaci ayi binciken gaggawa tare da daukar mataki don dakile faruwar hakan a gaba.
Wannan na zuwa ne bayan sojoji sun kai hari kan masu Maulidi a kauyen da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng