Shari’ar Kano: An Shiga Rudanin ‘Wasikar’ da Ake Zargin Dahiru Bauchi Ya Rubutawa Alkalai

Shari’ar Kano: An Shiga Rudanin ‘Wasikar’ da Ake Zargin Dahiru Bauchi Ya Rubutawa Alkalai

  • Shari'ar Kano ta je kotun koli, an fara jita-jitar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fito da wata wasika
  • A wasikar da ake ikirari, Shehin ya ja kunnen Alkalin Alkalai su yi gaskiya kan shari’ar zaben Kano
  • Dahiru Bauchi ya shaidawa duniya cewa bai fitar da jawabin komai a game da shari’ar jihar Kano ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano – Rade-radi yana yawo cewa Dahiru Usman Bauchi ya rubuta takarda zuwa ga Alkalin Alkalan Najeriya a game da shari’ar zaben Kano.

Rahotannin da ke yawo sun ce Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya tsoma baki a kan shari’ar zaben gwamnan jihar Kano da ke gaban kotun koli.

Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Bauchi ya nesanta kan sa daga siyasar Kano Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Daga baya mun fahimci babu wani kanshin gaskiya a takardar da ke yawo da sunan babban shehin darikar na Tijjaniya a Afrika ta yamma.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A takardar da da ake cewa Shehin malamin ya rubuta a daren ranar Asabar, ya nuna muhimmancin yin adalci a shari’ar zaben gwamnan.

Da gaske Dahiru Usman Bauchi ya rubuta wasika?

Legit ta tuntubi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta wayar salula domin jin gaskiyar lamarin.

Ba mu samu shehi a layinsa ba, amma na kusa da shi da ke kula da wayoyinsa sun tabbatar mana sun ga wannan takarda ta na yawo a yau.

Sai dai kamar kowa, gidan Shehin sun tabbatar mana babu abin da ya hada su da wannan wasika, ba daga wurin babban malamin ta fito ba.

Abin da wasikar karyar Sheikh Dahiru Bauchi ta kunsa

Dahiru Usman Bauchi ya nuna damuwarsa a game da abin da ya faru bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a watan Oktoba.

Alkalan kotun daukaka kara sun amince da hukuncin kotun korafin zabe wajen soke nasarar da hukumar INEC ta ba Abba Kabir Yusuf da NNPP.

Kara karanta wannan

Ba Dani Ba: Sheikh Dahiru ya yi martani kan wasikar da aka ce ya rubuta kan rikicin Abba da Gawuna

Ana ikirarin Shehin ya ce Kano cibiyar harkar addinin musulunci da kasuwanci ce a Arewa, ya kamata alkalai su tabbatar da zaman lafiyan jihar.

Takardar bogin ta kara da cewa an tunawa Alkalin alkalan kasar tashin hankalin da aka shiga lokacin yakin basasa a tsakanin 1967 zuwa 1970.

Maganar da aka alakanta da Dahiru Bauchi

“Saboda haka ina so in jaddada maku cewa dole ayi matukar adalci da gaskiya wajen sake duba hukuncin kotun daukaka kara.
Ka da a ji tsoro ko ayi son kai a kan zabin da mutane su ka yi domin gudun su ji cewa an sace kuri’unsu ko an yi watsi da su.
Mai shari’a, wannan ne ra’ayin duka malamai da masana da daukacin dattawan Arewa; haka kuma talakawan yankin da Najeriya.”

A wani faifen sauti da mu ka ci karo da shi a dandalin X, an ji muryar malamin musuluncin ya na musanya labarin da yake ta yawo.

Kara karanta wannan

"Kada ka tsoma baki a kitimurmurar da ke tsakanin Abba da Gawuna a Kano", Dattijan Yarbawa ga Tinubu

Amma kuma a wani bidiyo da ke Facebook, Naziru Tahir ya yi ikirarin shi ne ya fitar da wannan takarda da izinin Sheikh Dahiru Bauchi.

Ya dace malami irin Dahiru Bauchi ya tsoma baki siyasa?

Tun lokacin aka ji wasu sun fito suna sukan babban malamin da shiga harkar siyasa, wasu kuma sun ce kira da ayi gaskiya ba laifi ba ne.

A baya an saba jin malamai da masu mulki sun rubuta wasiku ga kotu yayin shari’a, wani lokaci Dahiru Bauchi ya kan yi maganar siyasa.

...Shari'ar Ike Ekweremadu a Ingila

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya aika takarda zuwa ga gwamnati da kotun Birtaniya a kan shari’ar Sanata Ike Ekweremadu.

Hakan ya faru ne lokacin da aka yi karar Ekweremadu a kan dashen koda ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel