Kotu Ta Raba Gardama Kan Shari’ar Neman Tsige Dan Majalisar APC, Ta Ba da Dalilai

Kotu Ta Raba Gardama Kan Shari’ar Neman Tsige Dan Majalisar APC, Ta Ba da Dalilai

  • Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Taraba a yau Asabar
  • Kotun da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar APC, Mark Useni a mazabar Donga/Takum/Ussa
  • Kotun yayin zamanta a yau Asabar 23 ga watan Disamba ta kori karar dan takarar NNPP, Rimamde Shawulu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta raba gardama a shari'ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Taraba.

Kotun yayin zamanta a yau Asabar 23 ga watan Disamba ta kori karar dan takarar NNPP, Rimamde Shawulu.

Kotu ta raba gardama kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya
Kotu ta yi hukunci kan shari'ar tsohon kakakinm Majalisar Taraba. Hoto: Mark Useni, Rimamde Shawulu.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kotun har ila yau, ta tabbatar da nasarar zaben dan takarar jam'iyyar APC, Mark Useni a mazabar Takum/Ussa/Donga.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutane 52 a hannun 'yan bindiga yayin wani artabu, an bayyana matakin gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma yi fatali ta karar inda ta ce babu gamsassun hujjoji da za su rusa zaben da ake magana a kai, cewar The Nation.

Da ya ke martani, Useni ya bayyana wannan nasara a matsayin karin kwarin gwiwar ci gaba da ayyukan alkairi a mazabar.

A watan Oktoba ce kotun zabe a Jalingo ta tabbatar da nasarar Useni tare da watsi da karar dan PDP, Istifanus Gbana da na NNPP da suka kalubalanci zaben.

Wane korafi 'yan takarar ke yi?

Masu korafin sun bukaci rusa zaben saboda rashin bin ka'idar dokokin zabe na hukumar INEC.

Sun kuma tabbatar da cewa Mark Useni bai samu ingantattu kuma mafi yawan kuri'u ba da za a sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe.

Tsohon kakakin Majalisar jihar bayan hukuncin ya tabbatar da cewa ya shiga matsi kan shari'ar zaben kujerar tashi, cewar Latest Nigerian News.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan nasarar gwamnan PDP a zaben 2023

Kotu ta yi hukunci kan zaben kakakin Majalisa

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan zaben kakakin Majalisar jihar Gombe, Abubakar Luggerewo.

Kotun ta tabbatar da zaben kakakin Majalisar wanda dan jam'iyyar APC ne a jihar Gombe.

Har ila yau, ta yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar PDP, Bashir Gaddafi a mazabar Akko ta Tsakiya saboda rashin hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.