Rikicin Siyasa Ya Rikide Bayan Dattawan Rivers Sun Maka Tinubu a Kotu Kan Abu 1 Tak, Sun Fadi Dalili

Rikicin Siyasa Ya Rikide Bayan Dattawan Rivers Sun Maka Tinubu a Kotu Kan Abu 1 Tak, Sun Fadi Dalili

  • Rikicin jihar Rivers ya sauya salo bayan dattawan jihar sun maka Shugaba Tinubu da Gwamna Fubara da kuma INEC a kotu
  • Dattawan sun maka su a babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan shiga yarjejeniya wacce ta sabawa dokar kasa
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake takun saka tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike wanda shi ne Ministan Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers – Yayin da rikicin jihar Rivers ke kara kamari, dattawan jihar sun maka Shugaba Bola Tinubu a babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Dattawan sun maka Tinubu ne a kotun saboda tilasta Gwamna Fubara na jihar da shiga yarjejeniya da Nyesom Wike, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya dira jihar Legas, an bayyana muhimmin abinda zai yi

Dattawan Rivers sun maka Tinubu a kotu kan dalili 1 tak
Rikicin siyasar jihar Rivers ya sauya salo. Hoto: Sim Fubara, Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Mene dalilin maka Tinubu a kotu?

Wannan na zuwa ne yayin da ake takun saka tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike wanda shi ne Ministan Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta tattaro cewa dattawa sun yi fatali da yarjejeniyar da Tinubu ya kulla inda suka ce ya sabawa kundin tsarin mulkin 1999.

Masu karar wanda mamban Majalisar jihar mai wakiltar mazabar Bonny, Victor Jumbo ya jagoranta sun hada da Sanata Bennett Birabi.

Su waye kuma aka maka a kotun bayan Tinubu?

Sauran sun hada da Sanata Andrew Uchendu da O. P Fingesi da Ann Kio Briggs da kuma Emmanuek Deinma.

Dattawan sun bukaci kotun ta yi bahasi ko ya dace Tinubu da Fubara da kuma Majalisar jihar su shiga yarjejeniyar wacce ta sabawa tsarin mulki.

Har ila yau, dattawan suka ce da Tinubu da Fubara dukkansu babu wanda ya ke da karfin ikon dakatar da INEC gudanar da zaben maye gurbin sauran 'yan Majalisar 27.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan PDP da APC da su ka halarci zaman sulhun da Tinubu yayi wa Wike da Fubara

Sauran wadanda aka maka a kotun sun hada da Ministan Shari'a da Gwamna Fubara da Ma'aikatar Shari'a da Majalisar jihar da kuma hukumar INEC.

An rushe Majalisar Rivers

A wani labarin, Yayin da rikicin siyasar jihar Rivers ke kara ta'azzara, an rushe Majalisar jihar kan wasu dalilai.

Hakan na zuwa ne yayin ake takun saka tsakanin Gwamna Sim Fubara da kuma mai gidansa, Nyesom Wike.

Rikicin ya haddasa wasu 'yan Majalisar jihar guda 27 sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel