Waiwayen Shekara: Jerin Yan Siyasar Najeriya Mafi Shahara a 2023

Waiwayen Shekara: Jerin Yan Siyasar Najeriya Mafi Shahara a 2023

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Sai mutum ya jajirce sosai ne yake tasiri a fagen siyasar Najeriya kuma ba dukkanin yan siyasa bane suke cimma haka a kowani zagaye na zabe.

Karfin ikon rinjayar masu jefa kuri'u da kawo kananan hukumomi a jihohi yana daga cikin yan tsirarun abubuwan da ke sa mutum ya ci gaba da tasiri a siyasance.

Fitattun yan siyasar Najeriya
Waiwayen Shekara: Jerin Yan Siyasar Najeriya Mafi Tasiri a 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Mr Peter Obi/Nyesom Wike -CON
Asali: Facebook

A wannan zauren, Legit Hausa ta lissafo jerin yan siyasa mafi tasiri a fadin kasar a 2023.

Shugaban kasa Bola Tinubu

Da kusan shekaru 20 yana gina alakar siyasa a fadin kasar, yana zuba jari a mutane da kafa tsarin siyasa, ba abun mamaki bane cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya ma babban zaben 2023 da kyau.

Kara karanta wannan

"Kudin ka mutuncin ka", Dino Melaye ya ba 'yan Najeriya shawarar su tashi su nemi arziki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lashe zaben shugaban kasa ba abu ne mai sauki ba kuma yin hakan a karo na farko da jam'iyyar siyasa da yan Najeriya suka cire tsammani da ita ba karamin abu bane.

Kwarewar Tinubu da dabarunsa na sulhu ba na wasa bane tunda har ya iya shawo kan Wike, jigo a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya yi masa aiki don ganin ya sha gaban Peter Obi, wanda ke jam’iyya daya da tsohon gwamnan na jihar Ribas.

Nyesom Wike

Ministan babban birnin tarayyam Nyesom Wike, yana daya daga cikin yan siyasa mafi tasiri a Najeriya yayin babban zaben 2023.

Dagewar da Wike ya yi cewa dole shugabanci ya koma kudu da rawar ganin da ya taka wajen nasarar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna cewa shi dan siyasa ne da ba za a iya watsi da shi ba.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan PDP da APC da su ka halarci zaman sulhun da Tinubu yayi wa Wike da Fubara

Kafin zaben shugaban kasa na 2023, Port-Harcourt ta zama sabuwar cibiyar siyasar Najeriya saboda yawan yan siyasar da suka ziyarci jihar Ribas don neman goyon bayan gwamnan wancan lokacin, jaridar Leadership ta rahoto.

Ba a bar yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi da Musa Rabiu Kwankwaso na NNPP a baya ba wajen kai ziyarar.

Hatta ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC sai da ya aika tawagarsa karkashin jagorancin gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu, na Ondo, Rotimi Akeredolu da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, don nema masa yardar Wike.

Peter Obi

Shigar Peter Obi takarar shugaban kasa na 2023 ya yi sanadiyar bayyanan gagarumar jam'iyyar adawa wacce ta girgiza yanayin siyasar Najeriya.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, zabukan baya a kasar ya kan kasance tsakanin jam'iyya mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ne. Amma Obi ya sauya tsarin a zaben da ya gabata.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi halin da ake ciki a bincike kan jefa Bam a taron Musulmai a Kaduna

Tsohon gwamnan na Anambra ya yi tasiri sosai wanda ya kai ga bayyanar tafiyar "Obidient" don yada manufarsa na inganta Najeriya. Tafiyar Obidient ta kalubalanci Obi don yin takara a zaben shugaban kasa na 2023.

Samun kuri'u sama da miliyan 6 a karkashin jam'iyyar da bata da tsari mai karfi da karfin aljihun da abokan hamayyarta ke da shi abu ne da ba a yi tsammani ba ga wanda ya shiga tseren shugabancin kasa a karo na farko.

Rabiu Musa Kwankwaso

Da kusan kuri'u miliyan biyar kuma na biyu a yawan al'umma a kasar, cin jihar Kano na da matukar muhimmanci ga kowani dan takara da ke son yin nasara a zaben shugaban kasa a Najeriya.

Ba cin jihar Kano kawai Kwankwaso ya yi ba a zaben shugaban kasa, ya kawowa jam'iyyarsa ta NNPP kujerar gwamna, sannan ta lashe mafi rinjayen kujeru a zabukan yan majalisun jiha da na tarayya.

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Buhari ya ci gyaran Shugaba Tinubu a kan abubuwa 2 da ya aikata a ofis

Ya tabbatar da cewar shine ke da Kano kuma tasirinsa a matsayin tsohon gwamna na nan daram-dam a duk jam'iyyar siyasar da zai fito.

Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 yana da tasiri sosai a bangaren siyasa tsawon shekaru da dama.

Atiku ya shiga harkar siyasar Najeriya tun a 1999 bayan an daura shi a matsayin mataimakin shugaban kasa na Olusegun Obasanjo saboda tasirinsa a matsayin jagoran tsarin siyasar marigayi Yar'adua a jihar arewa, rahoton Vanguard.

Bayyanansa yazo bayan ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa karkashin inuwar PDP a yunkurinsa na hudu.

Kamar yadda Premium Times ta rahoto, Atiku da yake zantawa da shugabanni kungiyoyin goyon bayansa 200, ya ce:

"Misali na yi takarar kujerar gwamna sau hudu kafin a karshe aka zabe ni."

Lalong ya magantu kan murabus dinsa

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

A wani labarin, mun ji cewa ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong ya sauka daga kujerarsa a hukumance a ranar Talata, 19 ga watan Disamba.

Kakakinsa, Simon Macham, Lalong ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng