‘Yan Kwankwasiyya da Masoyan Abba Sun Tashi da Azumi Domin Yin Nasara a Kotun Koli
- Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi kira ga ‘Yan Kwankwasiyya da NNPP su yi azumin nafila a ranar Alhamis
- Magoya bayan Abba Kabir Yusuf suna fatan hakan zai taimaka su iya samun galaba a gaban kotun koli
- Jam’iyyar NNPP ta rasa duka shari’o’in zaben gwamna da aka yi a kotu, tana tsoron rasa kujerarta a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda shi ne Darektan yada labarai a gidan gwamnatin Kano ya yi kira ga magoya bayan NNPP.
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa a Facebook, ya yi kira ga magoya bayan Abba Kabir Yusuf su dage da ibada domin nasara.
A yau ne kotun koli za ta fara sauraron shari’ar Mai girma Abba Kabir Yusuf da APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba Kabir Yusuf yana kokarin ya tsira da kujerarsa bayan Alkalan kotun daukaka kara da na korafin zabe sun ba APC nasara.
Dawakin Tofa ya ce ‘Yan darikar Kwankwasiyya magoya bayan Gwamnan Kano su tashi da azumi na musamman ganin cewa yau Alhamis.
Jami’in da ya samu karin matsayi kwanan nan ya ce wadanda su ka samu dama su yi dogara da azumin domin Allah SWT ya ba NNPP sa’a.
'Yan APC da NNPP sun dage da ibada a Kano
A shafin Facebook har ila yau, Sanusi Oscar ya kawo wani salon sallah na mutum miliyan guda da ya ce mabiya Kwankwasiyya su yi.
Kwanakin baya da ‘yan siyasa su ka kirkiro sallolin jam’i da nufin yin nasara a kotun zabe, malaman musulunci su nuna hakan bai da asali.
“Salam Yan uwa Yan Kwankwasiyya, magoya bayan Gwamnan Kano H.E. Abba Kabir Yusuf na ciki da wajen Kano.
"Ana bukatar ga masu dama, su dau azumin nafila gobe Alhamis tare da yin tawassuli da shi domin neman Allah ya taimake mu a kan shari'ar da ke gaban mu wadda za a fara gobe.
"Mun gode, Allah ya bar zumunci
"Naku. Sabature"
- Sanusi Bature Dawakin Tofa
Shari'ar zaben Gwamnan Kano Kano
Kuna da labarin yadda jam’iyyar NNPP ta rasa duka shari’o’in zaben gwamnan Kano da aka yi a kotun korafin zabe da kotun daukaka kara.
Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara zuwa kotun koli inda shari'ar zaben za ta kare.
Asali: Legit.ng