An Yiwa Laftanan, Manjo da Birgediya Janar Fiye da 100 Ritaya Daga Aiki a Gidan Soja

An Yiwa Laftanan, Manjo da Birgediya Janar Fiye da 100 Ritaya Daga Aiki a Gidan Soja

  • Sojojin kasa 113 da aka yi sallama da su a dalilin ritaya, an shirya walima domin jami’an da aka rasa
  • Ritayar da aka yi wa jami’an sojojin sun shafi Janar daya da wani Laftanan Janar da ake da shi a Najeriya
  • Manjo Janar da Birgediya Janar 111 sun yi ritaya, an nemi sojojin da ke bakin aiki su yi biyayya ga dokar kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Talata, 19 ga watan Disamba 2023, aka tabbatar da yi wa manyan Janarori ritaya daga aikin soja a Najeriya.

Punch da ta fitar da rahoton ta ce ritayar ta shafi cikakken Janar da Laftanan Janar guda.

Sojoji
Janar na Sojojin da aka yi wa ritaya Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Manjo da Birgediya Janar 111 sun bar aikin soja

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan PDP da APC da su ka halarci zaman sulhun da Tinubu yayi wa Wike da Fubara

Sauran wadanda aka yi bankwana da su cikin dakarun sojojin kasan sun hada da Manjo Janar 67 da kuma Birgediya Janar har 44.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya liyafa ta musamman domin karrama wadannan manyan jami’an sojoji da aka yi wa ritaya bayan tsawon shekaru suna aiki.

Babban Ministan tsaro, Muhammadu Abubakar Badaru ya yabawa kokarin da sojojin kasa su ke yi wajen kawo cigaban damukaradiyya.

Muhammadu Abubakar Badaru ya ce sojojin Najeriyan sun yi fice tare da zama abin misali cikin takwarorinsu a fadin yammacin Afrika.

An rahoto Ministan ya ce sauran kasashe za su iya koyi daga dakarun sojojin Najeriya.

A wani jawabi da ya fito daga Darektan hulda da jama’a na sojoji a X, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce Ministan ya yi kira ga sojoji.

Janar Onyema Nwachukwu ya ce an bukaci sojojin su zama masu biyayya ga kundin tsarin mulki kuma su karfafi mulkin farar hula a kasar.

Kara karanta wannan

Harin sojojin Najeriya kan farar hula: Miyetti Allah ta kafa wa Tinubu wani muhimmin sharadi

Daga lokaci zuwa lokaci, a kan yi wa jami’an sojoji ritaya saboda sun cika shekarun aiki ko idan ‘yan ajin bayansu sun samu karin matsayi.

Nuhu Ribadu ya je taron sulhu

Ana da labarin yadda mai girma shugaban kasa ya shiga ya fita domin sasanta Gwamna Sim Fubara da Nyesom Ezenwo Wike a Ribas.

Akwai sa hannun Nuhu Ribadu wanda shi ne Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro a takardar yarjejeniyar da aka amince a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel