Dalilin da Yasa Na Yi Murabus Daga Gwamnatin Tinubu, Lalong Ya Magantu
- Majalisar Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta kasance ba tare da daya daga cikin amintattun na hannun damansa ba, Simon Lalong
- A kwanan nan ne Lalong ya yi murabus daga mukaminsa na ministan kwadago da daukiar ma'aikata bayan da ya yi nasara a kotun daukaka kara inda ya koma majalisar dattawa
- Tsohon gwamnan na jihar Filato ya ce ya yi tuntuba da dama kafin ya yi murabus daga majalisar Tinubu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong ya yi murabus daga kujerarsa a hukumance a ranar Talata, 19 ga watan Disamba.
A cewar wata sanarwa daga kakakinsa, Simon Macham, Lalong ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya dauki matakin ne domin ya samu damar darewa kujerarsa a matsayin sanata mai wakiltan Filato ta kudu karkashin inuwar jam'iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarar Lalong a kotun daukaka kara
Lalong ya yi murabus ne sakamakon nasarar da ya samu a zaben sanata na ranar 25 ga watan Fabrairu, bayan kotun daukaka kara ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar 7 ga watan Nuwamba.
Hukuncin kotun ya sauya sanarwar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi a baya, inda ta ayyana Napoleon Bali na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Lalong ya karbi takardar shaidar cin zabe daga wajen INEC a watan jiya sannan a yanzu ya shirya kama aikinsa na sanata.
Mista Macham ya jaddada cewa zabin ministan na sauka daga mukaminsa na minista abu ne mai matukar nauyi.
Ba a dauki wannan mataki da wasa ba saboda amana da kwarin gwiwar da Shugaba Tinubu ya ba shi.
A baya ministan ya yi aiki a matsayin darakta janar na kwmaitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, inda ya taka muhimmiyar rawar gani wajen nasarar da APC ta samu.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta nakalto, sanarwar na cewa:
Sai dai kuma, bayan tuntuba mai yawa da mai girma shugaban kasa da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummata, ya zama dole gareni in ci gaba da zama a majalisar dattawa don ci gaba da ba da gudummawa ga ajandar sabunta fata na gwamnatin ka da kuma ci gaban dimokuradiyyar mu gaba daya."
Lalong ya yi alkawarin yin biyayya ga Tinubu
Mista Lalong ya yi godiya ga shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin aiki a majalisarsa da kuma irin goyon baya da jagorancin da ya samu a lokacin da yake rike da mukamin minista.
Yayin da yake a majalisar dattawa, ministan ya yi alkawarin biyayya, goyon baya, da bayar da hadin kai ga shugaba Tinubu, domin bayar da gudumawa ga ajandar sabunta fata da kuma ciyar da manufofin jam’iyyar APC gaba don samun hadin kai, ci gaba da wadata a Najeriya.
Sanarwar ta bayyana cewa sabon zababben Sanatan ya ziyarci majalisar ne domin mika takardar shaidar cin zabensa da kuma takardun da suka dace ga magatakardar majalisar.
Lalong ya dau rantsuwar aiki
A gefe guda, mun kawo a baya cewa tsohon gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya kama rantsuwar kama aiki a matsayin Sanata a jihar.
Lalong wanda shi ne tsohon Ministan Kwadago ya karbi rantsuwar ce a dakin Majalisar Dattawa a yau Laraba 20 ga watan Disamba a Abuja.
Asali: Legit.ng