Kano: Zanga-Zanga Ta Sake Barkewa a Kudancin Najeriya Kan Hukuncin Jihar, Sun Nemi Bukata Mai Girma
- Hausawa mazauna jihar Ogun sun fito zanga-zanga don nuna damuwa kan shari’ar jihar Kano da ake dako a wannan satin
- Masu zanga-zangar wadanda su ka hada da matasa da yara sun fito titunan garin Sagamu a yau Talata 19 ga watan Disamba
- Matasan sun fito ne a Sagamu da ke jihar tare da kiran Shugaba Tinubu da ya yi mai yiyuwa don dakile rikici a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun – Al’ummar Hausawa da ke Sagamu a jihar Ogun sun fito zan-zanga kan shari’ar zaben jihar Kano.
Masu zanga-zangar wadanda su ka hada da matasa da yara sun fito titunan garin ne a yau Talata 19 ga watan Disamba.
Mene matasan ke cewa kan shari'ar Kano?
Matasan sun bukaci Shugaba Tinubu ya saka baki don ganin an yi adalci a hukuncin kotu da ake dako a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bukaci shugaban ya tabbatar da yin adalci a shari’ar don dakile matsala wanda ka iya shafar har Kudancin kasar da su ke.
Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli kan shari’ar zaben jihar a ranar Alhamis mai zuwa, cewar Leadership.
Hausawan sun bukaci Kotun Koli da ta bai wa al’umma abin da su ka zaba a zaben da aka gudanar a watan Maris, cewar Punch.
Wane gargadi su ka tura ga Tinubu?
Sun kuma gargadi hukumomin da cewa za a iya rasa zaman lafiya idan har aka yi wani abu sabanin abin da ya kamata musamman a shari’ar.
Yayin da ya ke magana da manema labarai, daya daga cikin shugabannin taron, Alhaji Nasir Seriki-Kano ya bayyana dalilin wannan zanga-zangar.
Nasir ya ce sun fito ne don tunatar da Gwamnatin Tarayya kan cewa komai na iya faruwa idan ba a yi abin da ya dace ba a Kano.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wadansu mazauna jihar Oyo sun fito zanga-zanga don nuna damuwa kan hukuncin kotu a Kano, cewar Tribune.
Mazauna Oyo sun nuna damuwa kan shari'ar Kano
A wani labarin, Al’ummar Hausawa mazauna jihar Oyo sun fito zanga-zanga don nuna damuwa kan shari’ar zaben jihar Kano.
Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin shari’ar jihar Kano a ranar Alhamis mai zuwa.
Asali: Legit.ng