Wike vs Fubara: Jerin Yan Siyasan da Suka Sanya Hannu a Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Rivers

Wike vs Fubara: Jerin Yan Siyasan da Suka Sanya Hannu a Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Rivers

  • An cimma yarjejeniyar zaman lafiya domin dawo da al'amuran siyasar jihar Rivers kan hanya
  • A ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani a rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamnan jihar da magabacinsa
  • Yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin bangarorin biyu ta tabbata tare da sa hannun mutum bakwai da ke ƙunshe a cikin takardar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwanan nan ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kira taron masu ruwa da tsaki tare da Gwamna Siminalayi Fubara na Rivers, da tsohon gwamna Peter Odili, da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da wasu fitattun mutane.

An kammala taron tare da zartar da wasu muhimman ƙudurori guda takwas domin dawo da daidaito a siyasar jihar mai arziƙin man fetur.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa na kulla yarjejeniya 8 da Wike", Gwamna Fubara Ya Magantu

An cimma yarjejeniya kan rikicin Rivers
Yan siyasa bakwai suka sa hannu a yarjejeniyar Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nuhu Ribadu, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan kafafen sada zumunta ya fitar, Gwamna Fubara ya ƙuduri aniyar janye duk wani matakin shari’a da aka fara yi kan ƴan majalisar dokokin jihar waɗanda suka sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma ita ma majalisar dokokin jihar ta yanke shawarar dakatar da yunƙurin tsige Gwamna Fubara.

A wani ɓangare na yarjejeniyar, sun amince da ikon shugabancin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule da wasu ƴan majalisa 27.

Waɗannan ƴan majalisar sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC inda suka hada kansu da ɓangaren Wike.

Wasu fitattun mutane bakwai ne suka sanya hannu a cikin takardar yarjejeniyar domin tabbatar da zaman lafiya.

Waɗannan mutanen sun haɗa da:

1. Gwamna Sim Fubara

Gwamnan jihar Rivers dai ya kasance wanda rikicin siyasar jihar ya ritsa da shi a farkon mulkinsa, ko shekara ɗaya bai yi ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan yarjejeniya 8 da Tinubu ya cimmawa tsakanin Wike da Fubara

Kafin wannan yarjejeniya dai Fubara ya rasa ikon tafiyar da majalisar kwamishinoninsa yayin da ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 suka janye masa goyon bayansu tare da sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Rikicin ya kara ƙamari ne a lokacin da ƴan majalisar suka ki halartar taron gabatar da kasafin kuɗi na Gwamna Fubara.

2. Nyesom Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, shi ne ɓangare na biyu da ake rikicin da shi, inda ya yi kaca-kaca da wanda ya gaje shi, Gwamna Fubara.

Wike ya zargi gwamnan jihar Rivers da son ruguza tsarin siyasarsa na kusan shekaru goma.

An kuma sanya sa hannun tsohon gwamnan jihar Rivers a cikin takardar yarjejeniyar zaman lafiyan.

3. Ngozi Odu

Mataimakiyar gwamnan jihar Rivers, Ngozi Odu, ba ayi maganarta ba sosai a lokacin rikicin nan, domin yanayinta bai nuna ɓangaren da take goyon baya ba.

Sai dai, akwai sa hannunta a cikin yarjejeniyar wacce Shugaba Tinubu ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan abu 1

4. Kakakin majalisar dokokin Rivers

Shugaban majalisar dokokin Rivers, Martin Chike, shi ma rikicin siyasar jihar ya shafe shi.

Chike ya kuma sanya hannu kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya don maido da doka da oda a jihar.

5. Nuhu Ribadu (Mai bada shawara kan tsaro)

6. Shugaban PDP na Rivers

7. Shugaban APC na Rivers

Fubara Zai Sake Gabatar da Kasafin Kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara zai sake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 a gaban majalisar dokokin jihar.

Hakan dai na cikin yarjejeniyar da aka cimma domin sasanta rikicin da ke tsakaninsa da Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel