Tinubu Ya Saka Labule da Gwamnan PDP da Kuma Tsohon Gwamna, an Fadi Dalili

Tinubu Ya Saka Labule da Gwamnan PDP da Kuma Tsohon Gwamna, an Fadi Dalili

  • Yayin da rikicin siyasa ke kara ta'azzara a jihar Rivers, Bola Tinubu ya shiga ganawar sirri da Gwamna Fubara na jihar
  • Har ila yau, daga cikin wadanda su ke cikin ganawar akwai tsohon gwamnan jihar, Peter Odili da sauran masu ruwa da tsaki
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun matsala tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawar gaggawa da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Daga cikin mahalarta taron na sirri akwai tsohon gwamnan jihar, Peter Odili da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

Kara karanta wannan

APC ta yi nasara yayin da kotu ta dakatar da INEC kan sake zaben 'yan Majalisu 27, ta tura gargadi

Tinubu ya shiga ganawar sirri da gwamnan PDP a fadarsa da ke Abuja
Tinubu ya saka labule da Gwamna Fubara na jihar Rivers. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene dalilin taron Tinubu da Fubara?

A yanzu haka ana ganawar ce a fadar shugaban kasar da ke Ado Rock a birnin Tarayya, Abuja, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ganawar ba ta rasa nasaba da rikicin siyasa da ta ki ci ta ki cinyewa a jihar tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.

Gwamna Fubara shi ya jagoranci tawagar da su ka hada da tsohon gwamnan da kuma masu rike da masarautun gargajiya a jihar.

Ana sa ran Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ma zai halarci taron, cewar gidan talabijin na Channels.

Su waye su ka halarci taron da Tinubu?

Har ila yau, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila su ma sun halarci taron.

Wannan ba shi ne karon farko ba da Shuaba Tinubu ke shiga wannan rikicin don kawo maslaha a jihar.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da Wike ya yi abu 1 ana tsaka da rikicinsa da Gwamna Fubara

A farkon watan Oktobar wannan shekara sai da shugaban ya shiga tsakani amma daga baya rikicin ya sake rincabewa zuwa wani abu daban.

Shugaba tsagin Majalisar Rivers ya fadi dalilin sauya sheka

A wani labarin, Shugaban tsagin Majalisar jihar Rivers, Martins Chike Amaewhule ya bayyana dalilin komawarsu jami'yyar APC.

Amaewhule ya ce Tinubu ne ya ba su tabbacin haka inda ya ce shugaban ya kawo ayyukan ci gaba a yankinsu.

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a jihar tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel