Kano: An Yi Yarjejeniya da Abba Kabir Don Bar Masa Kujerarshi Saboda Ya Koma APC? Gaskiya Ta Fito
- Jam’iyyar APC ta yi martani kan zargin cewa akwai yarjejeniya da aka kulla tsakaninta da jam’iyyar NNPP
- An yi ta yada jita-jitar cewa akwai wata yarjejeniya da aka yi inda su ka amince za su bar wa Abba Kabir kujerarshi
- Shugaban jam’iyyar a jihar Kano, Abdullahi Abbas shi ya yi wannan martani a yau Lahadi 17 ga watan Disamba a kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi martani kan zargin yarjejeniya da jam’iyyar NNPP kan shari’ar zaben Kano.
Jam’iyyar ta ce babu inda su ka yi wata ganawa da NNPP don bar musu kujerar Abba Kabir da wasu sharuda, cewar The Nation.
Yaushe APC ta yi martani a Kano?
Shugaban jam’iyyar a jihar Kano, Abdullahi Abbas shi ya yi wannan martani a yau Lahadi 17 ga watan Disamba a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abbas ya ce babu inda Tinubu ya gana da ‘yan NNPP inda ya musu alkawarin bar wa Abba Kabir kujerarshi don ya koma APC, cewar Daily Trust.
Ya ce an kirkiri wannan zance ne kawai a bata wa Tinubu mai son dimukradiyya suna inda ya ce wasu shugabannin NNPP ne ke yadawa.
Mene martanin APC kan lamarin a Kano?
Ya ce:
“Mun samu wata jita-jita cewa shugabannin NNPP sun samu Tinubu da ya bar wa Abba Kabir kujerarshi don ya koma APC daga baya.
“Babu inda aka yi wannan ganawa da Tinubu ko wani shugaban NNPP, Bola mutum ne mai son ci gaban dimukradiyya da kuma bin doka a kasa.
“Tinubu ba zai taba hada baki ba don kawo rashin adalci ba ko kuma ya kwace nasarar da wasu su ka samu.”
Abbas ya kara da cewa jam’iyyar APC bata san komai game da wannan lamari ba inda ya ce za ta yi duk mai yiyuwa don yin nasara a Kotun Koli.
Ya bukaci dukkan magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu da kuma yin watsi da dukkan farfaganda da NNPP ke yadawa.
Lauyan Kano ya fadi yiyuwar nasarar Abba
A wani labarin, wani lauya mazaunin jihar Kano, Umar Hassan ya yi hasashen yiyuwar nasarar Gwamna Abba Kabir a jihar Kano.
Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a shari’ar zaben gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng