Kotu Ta Raba Gardama Kan Shari’ar da Ke Neman Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Ba da Dalilai

Kotu Ta Raba Gardama Kan Shari’ar da Ke Neman Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Ba da Dalilai

  • Kotun Daukaka Kara ta raba gardama kan shari’ar zaben dan Majalisar Tarayya a jihar Anambra a jiya Asabar
  • Kotun ta yi watsai da karar dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Ogbaru, Chukwuka Onyema saboda rahin gamsassun hujjoji
  • Mai Shari’a, M. I Sirajo ya yanke hukuncin ne a jiya Asabar 16 ga watan Disamba inda ya ce Onyema bai ba da gamsassun hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari’ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Anambra.

Kotun ta yi watsi da karar dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Ogbaru, Chukwuka Onyema saboda rashin gamsassun hujjoji.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Jigon LP ta bayyana wanda ya kamata Kotun Koli ta ayyana a matsayin gwamnan Kano

Kotu ta yi hukunci kan zaben Majalisar Tarayya a jihar Anambra
Kotu ta raba gardama kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Anamnbra. Hoto: Court of Appeal.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar LP, Afam Victor Ogene wanda ya samu nasara a kotun zabe, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari’a, M. I Sirajo ya yanke hukuncin ne a jiya Asabar 16 ga watan Disamba inda ya ce Onyema bai ba da gamsassun hujjoji ba.

Sirajo ya ce dalilin haka ne ya saka kotun tabbatar da zaben Afam kamar yadda kotun zabe ta yi a ranar 20 ga watan Oktoba.

Yayin da ke martani, Ogene ya bayyana wannan nasara a matsayin taimako daga ubangiji inda ya ce hakan ya kara masa kwarin gwiwa.

Wane martani dan Majalisar ya yi?

Ogene, wanda shi ne shugaban kwamitin makamashi ya ce:

“Kamar yadda na fada a baya tun da kotun zabe ta tabbatar da nasara ta, ubangiji ne ya ke taimako na kuma wannan shi ne zabin al’umma.

Kara karanta wannan

Kotu ta ayyana zaben Majalisar Tarayya a matsayin wanda bai kammala ba, ta ba da dalili

“Zan yi duk mai yiyuwa don sauke nauyin da aka daura mini a matsayin wakilin al’umma.”

A watan Oktobar wannan shekara, kotun zabe ta tabbatar da nasarar Ogene na jam’iyyar LP tare da fatali da karar dan jam’iyyar PDP, Chukwuka Onyema, cewar Leadership.

Kou ta yi hukunci kan zaben jihar Sokoto

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan zaben Majalisar Tarayya a jihar Sokoto a jiya Asabar.

Kotun ta ayyana zaben dan Majalisa, Umar Yusuf Yabo na mazabar Yabo/Shagari wanda bai kamala ba a jihar Sokoto.

Yayin hukuncin, kotun ta ba da umarnin sake zabe a mazabu 26 da ke mazabar a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.