Kotu Ta Yi Hukunci Tare da Umartan Kwace Motocin Tsohon Gwamnan APC Guda 50, Ta Kori Kararshi

Kotu Ta Yi Hukunci Tare da Umartan Kwace Motocin Tsohon Gwamnan APC Guda 50, Ta Kori Kararshi

  • Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Sokoto ta ba da umarnin kwace motoci guda 50 daga tsohon Gwamna Bello Matawalle
  • Wannan na zuwa ne bayan kotun ta yi watsi da korafe-korafen karamin Ministan kan cewa motocin ba mallakin gwamnatin jihar ba ne
  • Gwamnatin Dauda Lawal na zargin Bello Matawalle da makarrabansa da kwashe dukkan motocin gidan gwamnatin

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Babbar kotun Tarayya a jihar Sokoto ta yi watsi da karar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle kan mallakar motoci.

A watan Yuni ce rundunar 'yan sanda ta kai farmaki gidan tsohon gwamnan don kwato motoci da ake zargin Matawalle da wawushe su, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Waye zai yi nasara a kotu? Jigon siyasa ya hango abin da zai faru a shari'ar Abba da Gawuna

Kotu ta raba gardama kan shari'ar wawushe motocin gidan gwamnati da Matawalle ya yi
Kotu ta umarci kwace motoci 50 daga Bello Matawalle. Hoto: Dauda Lawal, Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke kan shari'ar?

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta ba da umarnin kwace motocin daga wurin tsohon gwamnan wanda yanzu shi ne karamin Ministan Tsaro a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hukuncin kotun, ta umarci kwace motoci guda 50 daga Matawalle wanda ake zargin mallakin gwamnatin jihar ce, cewar Leadership.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Zamfara, Bala Idris ya fitar a yau Litinin 4 ga watan Disamba.

Wane martanin Gwamna Dauda Lawal ya yi?

Idris ya ce kotun ta yi watsi da korafe-korafen Matawalle kan cewa motocin mallakkinsa ne inda ta umarci kwace su daga hannunsa.

Dauda Lawal na zargin Matawalle da mukarrabansa da kwashe dukkan motocin gidan gwamnatin ba tare da barin komai ba.

Gwamnatin jihar ta samu umarnin kotun Tarayya inda ta kwato motocin guda 50 daga tsohon gwamna Matawalle.

Kara karanta wannan

Kotun ta yi hukunci kan shari'ar Abba Kabir da Ado Doguwa, ta umarci biyan diyyar miliyan 25

Daga bisani, tsohon gwamnan ya garzaya babbar kotun Tarayya da ke Gusau inda ta mayar masa da motocin.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar gwamnan Zamfara

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar Zamfara.

Kotun da ke zamanta Abuja ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba inda ta umarci sake zabe a kananan hukumomi uku.

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle shi ke kalubalantar zaben Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel