Daga Hawa Mulki, Mukaddashin Gwamnan APC Ya Yi Wani Abu 1 da Ya Tayar da Hankula
- Muƙaddashin gwamnan jihar Ondo ya fara gadan-gadan babu kama hannun yaro bayan ya karɓi ragamar mulkin jihar
- Lucky Aiyedatiwa ya bayar da umarnin kulle asusun ƙananan hukumomin jihar sai abin da hali ya yi
- Wannan matakin ya sanya tsoro a tsakanin shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin kan yiwuwar za a kore su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Akwai tashin hankali a tsakanin sabbin shugabannin riko na ƙananan hukumomi 18 da kuma shugabannin cigaban ƙananan hukumomi 33 kan cewa mukaddashin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, zai kore su.
Tsoron ya taso ne biyo bayan rufe asusun ƙananan hukumomin da Aiyedatiwa ya yi, cewar rahoton The Nation.
Mukaddashin gwamnan ya kuma shaidawa sabbin shugabanin da aka ƙirƙira da kada su buɗe sabbin asusu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata wasika zuwa ga ƙananan hukumomin na cewa:
"Masu girma shugabannin ƙananan hukumomi, mai girma muƙaddashin gwamnan jihar Ondo ya ba da umarnin a dakatar da duk wani abu da ake kashewa a asusun ƙananan hukumomi, kada a sanya hannu a kan caki, kada a canja sa hannu, ba za a cire kowane irin kuɗi ba har sai an ba da umarni."
"Da fatan za a bi umarni kuma a kiyaye."
Meyasa Aiyedatiwa ya kulle asusun?
Ɗaya daga cikin shugabannin riƙon wanda ya tabbatar da rahoton da aka sakaya sunansa ya ce hakan yana da ban tsoro.
Shugaban rikon ya ce Aiyedatiwa ya ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da ƙarfin mulkinsa bisa ga hangen nesansa tare da nuna cewa shi ne yanzu a kan mulki
A kalamansa:
"Eh, ya kulle asusun ƙananan hukumomi. Yana yin haka ne domin ganin shugabannin riƙo sun faɗo a kan layi gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a shekara mai zuwa. Ya yi imanin an karkatar da asusun ƙananan hukumomi."
Bayan kulle asusun ƙananan hukumomin, Aiyedatiwa ya ba da umarnin cewa mataimakin shugaban ma’aikata, Omojuwa Olusegun, shi ne zai riƙa shiryawa tare da rattaɓa hannu kan ayyukansa a hukumance a halin yanzu.
Aiyedatiwa Ya Zama Mukaddashin Gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Ondo ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar.
Majalisar ta bayyana hakan ne bayan ta samu wasiƙa daga Gwamna Rotimi Akeredolu wanda ya koma ƙasar Jamus yin jinya.
Asali: Legit.ng