Shugaba Tinubu Ya Gana da Jakadun Wasu Kashe 3 a Aso Villa, Ya Buƙaci Su Yi Manyan Abubuwa 2

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jakadun Wasu Kashe 3 a Aso Villa, Ya Buƙaci Su Yi Manyan Abubuwa 2

  • Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin jakadun wasu ƙasashe a Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Jumu'a
  • Shugaba Tinubu ya buƙaci su lalubo sabbin hanyoyin kasuwanci kana ya basu tabbacin za a saki kuɗaɗensu da suka maƙale
  • Tinubu ya jaddada cewa Najeriya gida ce kuma a shirye take ga duk masu son zuba hannun jari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci jakadun kasashen waje da ke Najeriya da su ba da fifiko wajen binciko sabbin hanyoyin kasuwanci.

Shugaban ya kuma roƙe su da su yi amfani da waɗanan hanyoyin wajen faɗaɗa kasuwanci a tsawon lokacin da zasu kwashe suka gudanar da ayyukansu a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Jakadun Wasu Kasashe a Villa, Ya Ba Su Umarni Kan Abu 2 Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya yi wannan kalamai ne ranar Jumu'a, 15 ga watan Disamba, 2023 yayin da ya karɓi bakuncin sabbin jakadun da wasu ƙasashe suka turo a Villa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation da ruwaito, jakadun da suka gana da Tinubu sun haɗa da na ƙasar Hungary, Lorand Endreffy; jakadan Ruwanda, Christophe Bazivamo da na Ukraine, Ivan Kholostenko

Shugaban Kasar ya kuma baiwa masu zuba jarin kasashen waje tabbacin cewa zasu samu kuɗin da suke tsammani da riba kuma za a daidaita tsarin haraji.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Jumu'a, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Shugaba ya baiwa masu zuba hannun jari tabbaci

Da yake jawabi yayin da ya karɓi bakuncin jakadan Ruwanda, Bola Tinubu ya ce kuɗaɗen da ake ta kace-nace da suka maƙale nan ba da jimawa ba za a sakar masu haƙƙinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bada mamaki kwana daya bayan miƙa kasafin kuɗin 2024 ga majalisa

Shugaba Tinubu ya ce:

"Mu ƴan gida daya ne a nahiyar mu. Za mu ci gaba da inganta dimokuradiyya da shugabanci na gari, kofa ta a bude take, kuma ministan harkokin waje da shugaban ma'aikata suna nan a koda yaushe."
“Don share muku tantama, mun yi nisa a aiki kan matsalolin biyan haraji sau biyu, kuma za a daidaita su yadda ya kamata domin mu maida hankali ga ci gaban kasuwanci. Najeriya gida ce ga masu zuba jari.”

Ana zargin Tinubu da goyon bayan Wike a rikicin Ribas

A wani rahoton na daban Ƙungiyar kabilar Ijaw ta ƙasa (INC) ta ce Bola Tinubu ya yi shiru game da rikicin da ministan Abuja ya tayar a Ribas saboda yana goyon bayansa.

Shugaban ƙungiyar ƴan kabilar Ijawa ta ƙasa INC, Farfesa Benjamin Okaba ya yi zargin cewa Tinubu ya rungume hannu, ya ki jan kunnen Wike kan rikicin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel