Gwamnan PDP da Ke Tsaka Mai Wuya Ya Samu Natsuwa Bayan ’Yan Majalisun Tarayya Sun Yi Masa Abu 1 Tak
- Manyan ‘yan Majalisar Tarayya guda biyu sun yi tattakin nuna goyon baya ga Gwamna Fubara na jihar Rivers a yau Juma’a
- ‘Yan Majalisar guda biyu sun yi fito tattakin ne tare da matasan kungiyar Ijaw don nuna goyon bayansu ga Gwamna Fubara
- Wannan tattakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa da ta ki cit a ki cinyewa a jihar tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers – Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana a jihar Rivers, Gwamna Fubara ya kara samun kwarin gwiwa.
Mambobin Majalisar Tarayya guda biyu ne su ka fito tattaki tare da matasa don nuna masa goyon baya.
Mene dalilin tattakin 'yan Majalisar?
‘Yan Majalisun sun hada da Awaji-Inombek Abiante da kuma Boma Goodhead wanda su ka yi tattakin har zuwa gidan gwamnatin jihar Rivers.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, ‘yan Majalisun sun samu tarbar dubban matasa da su ka hada da Kungiyar Matasan Ijaw a jihar, cewar Channels TV.
Abiante ya na wakiltar mazabar Andoni/Opobo/ Nkiru a Majalisar Tarayya yayin da Goodhead ke wakiltar mazabar Asari-Toru/Akuku-Toru.
Wannan tattakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa da ta ki ci ta ki cinyewa a jihar tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.
Mene silar rikicin jihar Rivers?
Tun bayan fara rikicin, a yanzu haka kusan kwamishinoni tara ne su ka yi murabus a gwamnatin Siminalayi Fubara.
Wadanda su ka yi murabus din na daga cikin wadanda ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, cewar Daily Post.
A rahoton da mu ke samu dazu, Gwamna Fubara ya kalubalanci dukkan kwamishinoni da ke yi Wike biyayya su yi murabus.
An rushe Majalisar jihar Rivers
A wani labarin, da safiyar ranar Laraba ce aka wayi gari da rushe Majalisar Dokokin jihar Rivers.
Wannan lamari bai rasa nasaba da rikicin siyasa da ke ci gaba da ruruwa a jihar tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.
Sai dai gwamnan jihar ya bayyana cewa an rushe Majalisar ce don yin gyara na musamman bayan abin fashewa ya taba bangaren Majalisar.
Asali: Legit.ng