Gwamnan PDP ya ɗau zafi, ya umarci wasu kwamishinoni su yi murabus nan take

Gwamnan PDP ya ɗau zafi, ya umarci wasu kwamishinoni su yi murabus nan take

  • Rikicin siyasar jihar Ribas tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike ya shafi manyan kusoshin gwamnati mai ci a jihar
  • Zuwa yanzu, kwamishinoni bakwai waɗanda ke goyon bayan tsohon gwamna Wike, sun yi murabus daga kan muƙamansu
  • A wani sabon shafi da rikicin ya buɗe, Gwamna Fubara ya umarci dukkan waɗanda Wike ya naɗa su bi sahun yan uwansu nan take

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya umarci dukkan kwamishinonin da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya naɗa su miƙa takardun murabus.

Gwamna Fubara da Wike.
Yanzun nan: Gwamnan PDP ya ɗau zafi, ya umarci wasu kwamishinoni su yi murabus nan take Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Wannan umarni ne na zuwa ne bayan kwamishinoni takwas daga cikin 18 sun yi murabus daga gwamnatin Fubara zuwa yau Jumu'a, 15 ga watan Disamba, 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya maida zazzafan martani yayin da ake shirin tsige shi daga kan mulki

Gwamnan ya umarci kwamishinonin Wike su yi murabus yau Jumu'a ko kuma a kore su daga aiki ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai amfani da kafar sada zumunta watau X wanda aka fi sani da Twitter, Omotayo Williams, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa.

Williams ya wallafa a shafinsa cewa:

"Labari da zafinsa, yanzu haka an umarci dukkan kwamishinonin da Wike ya naɗa su hanzarta yin murabus yau ko kuma a kore su daga aiki ranar Litinin mai zuwa."
"Ya zuwa yanzu kwamishinoni 10 ne suka yi murabus daga maƙamansu, tsarin Legas na iya aiki a kasar Yarbawa ne kawai, Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas ba zasu lamurta ba."

Yan siyasa a yankin Wike sun koma bayan Fubara

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tabbatar da barin Ciyamomi 21 da Kansiloli 239 ofisoshinsu, ya fadi dalili

Wannan na zuwa ne bayan jiga-jigan yan siyasa daga gundumomi 17 na ƙaramar hukumar Obio/Akpor, yankin da Wike ya fito sun marawa Gwamna Fubara baya.

Ƙusoshin siyasar sun jaddada goyon bayansu ga Fubara yayin da rikici ke ƙara tsnaanta tsakaninsa da Ministan Abuja.

Ƙarin kwamishinoni biyu sun yi murabus a Ribas

Rahotan da Legit Hausa ta samu yanzu na nuni da cewa wasu kwamishononi biyu sun yi murabus daga gwamnatin jihar Rivers.

Ajiye aikin kwamishinonin biyu a safiyar yau na nuni da cewa Gwamna Fubara ya rasa kwamishinoni shida daga Alhamis zuwa Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262