Jam’iyyar APC Ta Dena Boye Boye Ta Yi Wa Ministan Tinubu Tayin Da Zai Jawo Ya Bar PDP
- Jam’iyyar APC ta yi wa Nyesom Wike tayin shugabanci a jiharsa ta Ribas idan har ya rabu da PDP
- Shugaban rikon kwarya na APC a Ribas ya ce za su so ministan na Abuja ya shigo tafiyarsu a siyasa
- Zuwa yanzu Wike bai nuna yana da niyyar barin PDP ba duk sabaninsa da Siminalayi Fubara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - APC mai rike da mulkin kasa ta kara kaimi wajen ganin ta dauke Nyesom Wike daga jam’iyyar hamayya watau PDP.
Labari ya zo daga Daily Trust cewa shugabannin jam’iyyar APC sun yi wa Nyesom Wike alkawarin shugabanci idan ya bar PDP.
Jam’iyyar APC ta rabawa Nyesom Wike hankali
Da zarar babban ministan harkokin Abujan ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP, shi za a damkawa ragamar 'yan APC a jihar Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan na Ribas ya dage cewa ba zai bar jam’iyyarsa ta PDP ba duk da rikicin da ake yi da shi tun kafin zaben 2023.
Wike ya nemi tikitin takarar shugaban kasa amma Atiku Abubakar ya doke shi, hakan ta sa ya goyi bayan Bola Tinubu da APC.
A sakamakon gudumuwar da ya bada ne Wike ya zama Ministan Abuja a gwamnatin APC.
Rigimar Wike v Fubara ta barka PDP
Rigimar Mista Wike da Gwamna Siminalayi Fubara ta sa shugabannin jam’iyyar APC sun sake samun damar zawarcin ministan.
Shugaban rikon kwarya na APC a Ribas, Tony Okocha ya ce suna so Nyesom Wike ya shigo jam’iyyar domin su iya karbe mulki.
"Muna so APC ta yi nasara a Ribas wannan karo, kuma idan shi (Wike) ya zo, zai zama shugaban jam’iyya a jihar."
- Tony Okocha
APC da PDP suna neman iko da majalisar Ribas
An rahoto Tony Okocha yana cewa zaman da ‘yan majalisar Ribas su ka yi ba tare da ‘ya ‘yan APC ba, duk aikin banza ne kurum.
A haka ne Simi Fubara ya sa hannu a kasafin kudin da ya gabatarwa mutum biyar.
Mutanen Wike za su tsige gwamna?
Rahoto ya zo da ya tabbatar da cewa shirin tsige Gwamnan Ribas ne ya yi sanadiyyar da ‘yan majalisa suka sauya sheka zuwa APC.
A cewar wani ‘dan majalisar dokokin Ribas, duk abin da ake yi Nyesom Wike bai bar PDP ya shigo jam’iyyar APC mai mulki ba tukun.
Asali: Legit.ng