Yanzu: Tinubu Ya Yi Kokarin Sulhu Tsakanin Wike da Fubara, APC Ta Yi Karin Bayani
- Al’ummar jihar Ribas suna fama da rikicin siyasa da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar
- Yayin da yawancin yan majalisar jihar ke biyayya ga tsohon Gwamna Nyesom Wike, yan tsiraru ne ke tare da gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara
- Sai dai kuma, jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta jaddada cewar yunkurin Shugaban kasa Tinubu na sulhunta Wike da yaronsa a siyasa, Fubara ya ci tura
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai zauna ba a kan rikicin da ya dabaibaye jihar Ribas.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, shugaban riko na jam'iyyar APC a jihar Ribas, Tony Okocha, ya ce yunkurin shugaba Tinubu na kawo karshen rikici tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike ya rushe yayin da rikicin jihar ya ci gaba.
Ku tuna cewa a kwanan nan ne Tinubu ya gana da Wike da Fubara a fadar shugaban kasa da ke Abuja, domin kawo zaman lafiya tsakanin yan siyasar biyu a jihar, TVC News ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma a kwanaki hudu da suka gabata, rikicin ya dauki sabon salo da rushe ginin majalisar dokokin jihar da kuma sauya shekar yan majalisa 27 masu biyayya ga Wike, zuwa APC.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a sakatariyar APC na kasa a ranar Alhamis, a Abuja, bayan abun da ya faru a jihar, Okocha ya ce:
"Ban kasance a cikinsa ba, amma koma menene dai, ya lalace, kuma an karya shi ba tare da sulhu ba."
Ya kuma ce yan majalisar dokokin jihar hudu karkashin jagorancin Edison Ehie, wadanda suka zauna suka aiwatar da kasafin kudin da gwamnan jihar Fubara ya gabatar musu na shekarar 2024, sun aikata ba daidai ba, yana mai cewa matakin da suka dauka ba zai yi tasiri ba.
Okocha ya ce APC na zawarci Wike don ya dawo jam'iyyar yana mai cewa da zaran ya zama dan APC, zai zama shugaban jam'iyyar a jihar.
Gwamnatin Tinubu ta kitsa rikicin Ribas?
A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, ta ce ba ta da hannu a rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Rivers.
Rikicin siyasar dai ya shafi Gwamna Siminalayi Fubara, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja da ƴan majalisar dokoki masu biyayya ga tsohon gwamnan Rivers.
Asali: Legit.ng