Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Sanatan PDP, Ta Ci Tarar Dan Takara

Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Sanatan PDP, Ta Ci Tarar Dan Takara

  • Kasa da mako daya bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara, Kotun Koli ta sake raba gardama ta karshe a shari'ar Abia ta Tsakiya
  • Kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar PDP, Austin Akobundu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar
  • Har ila yau, kotun ta yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar LP, Darlington Nwokocha saboda rashin kasancewa dan jami'yya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli da ke zamanta a birnin Abuja ta raba gardama kan shari'ar zaben Abia ta Tsakiya.

Kotun ta tabbatar da dan takarar jam'iyyar PDP, Austin Akobundu a matsayin wanda ya lashe zaben, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shari'ar Kano: Lauya mazaunin Kano ya yi hasashen damar Abba Kabir a Kotun Koli

Kotun Koli ta raba gardama ta karshe kan shari'ar Sanatan Abia ta Tsakiya
Kotun Koli ta yi hukuncin karshe kan shari'ar Abia ta Tsakiya. Hoto: Austin Akobundu, Darlington Nwokocha.
Asali: Facebook

Wane hukucin kotun ta yanke a Abuja?

Yayin hukuncin a yau Talata 12 ga watan Disamba, kotun ta yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar LP, Darlington Nwokocha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta wallafa a shafin X a yau Talata 12 ga watan Disamba.

Nwokocha ya kalubalanci hukuncin Kotun Daukaka Kara ce da ta ce jami'yyarsa ba ta zabe shi a matsayin dan takara ba.

Wane mataki kotun ta dauka?

Kotun ta kuma ci tarar Nwokocha naira miliyan biyu wanda jimillar ya kai miliyan bakwai da Nwokocha zai biya Austin Akobundu.

Wannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben a Abuja.

Kotun ita ma ta tabbatar da nasarar Austin Akobundu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Majalisar Dattawa.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotu Daukaka Kara ta sanya ranar yanke hukunci a shari'ar zaben manyan sanatocin Arewa

Kotun ta yi hukunci kan shari'ar zaben Sanatan Abia ta Tsakiya

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a shari'ar zaben Sanatan Abia ta Tsakiya da ake kan yi.

Kotun ta tabbatar da nasarar da dan takarar jam'iyyar PDP, Austin Akobundu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Har ila yau, kotun ta yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar LP, Darlington Nwokocha saboda rashin kasancewa dan jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.