Yayin da Ake Rikicin Siyasa, Kotu Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Kakakin Majalisar PDP, Ta Yi Gargadi

Yayin da Ake Rikicin Siyasa, Kotu Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Kakakin Majalisar PDP, Ta Yi Gargadi

  • Kotun da ke zamanta a birnin Port Harcourt ta yi hukunci kan dambarwar siyasa a jihar Rivers kan shugabancin Majalisar
  • Babbar Kotun ta tabbatar da Edison Ehie a matsayin halastaccen kakakin Majalisar jihar bayan tumbuke shi a kwanakin baya
  • Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Majalisu 27 daga cikin 32 su ka sauya sheka zuwa APC daga jami'yyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Babbar Kotu a jihar Rivers ta yi hukunci kan sahihancin shugabancin kakakin Majalisar jihar, Edison Ehie.

Kotun ta tababar da Edison Ehie a matsayin halastaccen kakakin Majalisar jihar bayan kokarin tumbuke shi da Majalisar ta yi.

Kou ta yi hukunci kan shari'ar kakakin Majalisar jihar Rivers
Kotu ta raba gardama a shari'ar kakakin Majalisar jihar Rivers. Hoto: Sim Fubara, Edison Ehie.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Rivers?

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Mahara sun sace babban Sarki bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin hana garkuwar

Edison na daga cikin 'yan Majalisar guda hudu da ke tare da Gwamna Siminalayi Fubara a jihar yayin da ake ci gaba da rikici, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da rikicin siyasa ta barke a jihar, Majalisar ta tumbuke shi a matsayin shugaban masu rinjaye inda daga bisani aka zabe shi a matsayin shugaban Majalisar.

Kotun ta kuma dakatar da Martins Amaewhule da Dumle Maol da ci gaba da kiran kansu a matsayin kakakin Majalisar da kuma mataimaki a jere.

Wane gargadi kotun ta bayar?

Har ila yau, kotun ta kuma tura sakon gargadi kan amfani da 'yan ta'adda da jami'an 'yan sanda wurin shiga Majalisar da karfi, cewar Tori News.

'Yan Majalisar da ke goyon bayan Nyesom Wike wanda a yanzu shi ne Ministan Abuja a baya sun dakatar da Ehie a matsayin shugaban masu rinjaye.

Kara karanta wannan

Atiku ya magantu kan kin sakin bayanan karatunsa, ya dauki zafi

Wannan na zuwa ne bayan 'yan Majalisu a jihar guda 27 daga cikin 32 sun sauya sheka zuwa APC daga PDP.

Fubara ya shiga ganawar gaggawa

A wani labarin, Gwamna Siminalayi Fubara ya shiga ganawar gaggawa da majalisar zartarwa kan rikicin siyasa a jihar.

Wannan na zuwa yayin da rikicin siyasar jihar ke kara kamari bayan sauya shekar 'yan Majalisa zuwa APC daga PDP.

Ana zargin 'yan Majalisar da su ka sauya shekar na da alaka da Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda kuma shi ne uban gidan Gwamna Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.