Cikakken Sunayen Jiga-jigan APC da Ke Dakon Kujerar Minista Lalong Idan Ya Koma Sanata
Jiga-jigan jami'yyar APC a jihar Plateau sun fara nuna kwadayinsu kan neman kujerar Sanata Simon Lalong.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
A kwanakin nan Lalong ya ce bai yanke shawara ba kan ci gaba da zama a matsayin Minista ko kuma Sanata a Najeriya.
Jiga-jigan APC da ke neman kujerar Lalong
Lalong dai ya yi nasara a Kotun Koli bayan ya samu mukamin Minista a gwamnatin Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta jero muku wasu daga cikin masu son gadar kujerar tashi.
1. Farfesa Sale Kanam
Ana hasashen Kanam wanda tsohon shugaban karamar hukumar Kanam ne zai iya samun wannan dama ta kujerar Minista.
Farfesan na samun goyon baya daga Yusuf Gagdi da ke wakiltar mazabar Kanam/Pankshin/Kanke a jihar.
2. Farfesa Dakas Dakas
Dakas wanda tsohon kwamishinan Shari'a ne a mulkin tsohon Gwamna Lalong zai iya samun damar maye gurbin mai gidansa.
Masana sun ce kwarewar Dakas a bangaren Shari'a da kuma gudunmawar da ya bayar wurin sauya kundin tsarin jami'yyar ka iya ba shi dama.
3. Farfesa Danladi Atu
Tsohon Sakataren Gwamnatin Lalong ya na samun goyon baya daga mai gidansa.
Sai dai masana sun ce rashin samun goyon bayan jama'a idan aka kwatanta da sauran na iya kawo masa cikas a mukamin.
4. Farfesa Garba Sharabutu
Sharabutu wanda shi ne sakataren hukumar ARCN ana hasashen zai iya maye gurbin tsohon gwamnan jihar, Simon Lalong.
5. Komsol Alpanson
Alpanson wanda tsohon dan Majalisar Tarayya ne ka iya gadar kujerar ganin yadda ya ke da mutane a jihar.
Sai dai wasu sun yi korafin cewa zai iya rasa damar saboda rashin goyon bayan dan takarar APC a jihar.
6. Festus Fuanter
Festus shi ne mataimakin sakataren APC ta kasa wanda ke da hasken samun mukamin ganin yadda ya ke da alaka mai karfi da shugabannin jam'iyyar ta kasa.
7. Rufus Bature
Bature wanda shi ne shugaban jam'iyyar APC a jihar wanda magoyin bayan Tinubu ne na hakika zai iya samun damar gadar kujerar Lalong, cewar Daily Trust.
8. Bashir Musan Santi
Tsohon Sakataren jam'iyyar APC, Santi da kuma Sani Mudi, tsohon hadimin Lalong da su ka fito daga Jos ta Arewa ka iya samun kujerar Minista.
Lalong ya fara kokwanto kan kujerar Minista
A wani labarin, Ministan Kwadago Simon Lalong na tunanin barin kujerar Minista.
Lalong ya bayyana cewa ya shiga rudani da rashin tabbas kan wace kujera zai zaba.
Asali: Legit.ng