Kotun Koli: Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe Kan Takkadamar Zaben Kano

Kotun Koli: Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe Kan Takkadamar Zaben Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano na daukaka kara kan tsige shi da Kotun Daukaka Kara ta yi a watan Nuwamba
  • Gwamnan wanda ya kasance jigon NNPP ya tunkari Kotun Koli ta Najeriya bayan Kotun Daukaka Kara ta bada masa kasa a idanu
  • Yusuf na da kwarin gwiwar cewa Kotun Koli za ta yi watsi da hukuncin kotuna biyu da suka tsige shi, amma Primate Elijah Ayodele na ganin lamarin ya yi tsami

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Primate Babatunde Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya yi martani kan hukuncin da Kotun Koli za ta yanke a kan takkadamar zaben gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Shari'ar Kano: Lauya mazaunin Kano ya yi hasashen damar Abba Kabir a Kotun Koli

Primate Ayodele ya bukaci dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, da ya ci gaba da neman taimakon Allah domin samun makoma mai kyau a Kotun Koli.

Ayodele ya magantu kan zaben Kano
Kotun Koli: Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe Kan Takkadamar Zaben Kano Hoto: H.E Dr Nasir Yusuf Gawuna, Abba Kabir Yusuf, Primate Babatunde Elijah Ayodele
Asali: Twitter

Kano: "APC sun kwallafa rai tana shiri sosai", Ayodele

Kamar yadda malamin addinin ya bayyana, jam'iyyar APC da dan takararta, Nasiru Gawuna, sun kwallafa rai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayodele ya ce:

“A Kano Allah na iya canza ta idan an nemi taimakon Allah. Idan ba haka ba, APC za ta samu. Suna cikin shiri sosai.”

Lauya ya yi hasashe kan shari'ar zaben Kano

A gefe guda, wani babban lauya da ke jihar Kano, Umar Sa’ad Hassan ya yi hasashen abin da zai faru a shari’ar zaben jihar Kano.

Hassan ya bayyana yadda Gwamna Abba Kabir zai iya rasa dama a hukuncin Kotun Koli da ake dako a jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano ya bayyana gaskiyar zaman Abba 'dan NNPP kafin hukuncin kotun koli

Gwamnan ya daukaka kara ne bayan kotu ta sake rusa zabensa da aka gudanar a watan Maris.

NNPP ta magantu kan shirin yan Kwankwasiyya

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi watsi da zargin cewa jam’iyyar da 'yan Kwankwasiyya na shirin mamaye kotun koli da ofisoshin jakadancin kasashen waje a Najeriya.

Jam'iyyar NNPP ta bayyana zargin da ake mata da wani babban tuggu da bara gurbin tunani na wasu gamayyar ƙungiyoyin fararen hula, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng