Yanzu: Kotu Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci a Shari’ar Zaben Manyan Sanatocin Arewa

Yanzu: Kotu Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci a Shari’ar Zaben Manyan Sanatocin Arewa

  • Yayin da ake dakon shari’ar sanatoci biyu a jihar Sokoto, Kotun Daukaka Kara ta sanya ranar raba gardama a shari’ar
  • Kotun ta sanya yau Asabar 9 ga watan Disamba a matsayin ranar yanke hukuncin shari’ar Sanata Aminu Tambuwal da kuma Aliyu Wamakko
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kotun ta fitar wanda kakakin jam’iyyar PDP, Hassan Sanyin Lawal ya tabbatar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukuncin shari’ar zaben Sanata Aliyu Wamakko da Aminu Waziri Tambuwal.

Kotun ta sanya yau Asabar 9 ga watan Disamba a matsayin ranar yanke hukuncin shari’ar tsaffin gwamnonin biyu.

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci a zaben Majalisar Dattawa a Sokoto
Kotu ta shirya yanke hukunci a shari'ar zaben Majalisar Dattawa. Hoto: Court of Appeal.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta bayyana hukuncin da ya kamata Kotun Koli ta yanke a shari'ar jihar Kano

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kotun ta fitar ta wanda wakilin Tribune ya samu daga kakakin jam’iyyar PDP, Hassan Sanyin Lawal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsaffin gwamnonin da aka sanar sun lashe zaben sun samu nasara a kotunan zabe da aka gudanar a kwanakin baya.

Tambuwal da Wammako da ke wakiltar Sokoto ta Kudu da kuma Sokoto ta Arewa a jere sun yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Yadda hukuncin kotun zabe ta kaya a baya?

Wamakko wanda dan jam’iyyar APC ne ya yi nasara kan tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mannir Dan’iyya na jam’iyyar PDP.

Yayin da Tambuwal wanda ke jam’iyyar PDP ya yi nasara kan dan takarar APC, Ibrahim Danbaba Danbuwa, cewar Newstral.

Wannan na zuwa ne bayan dakon hukuncin kotun a shari'ar zaben jihar Kano da aka rusa zaben Abba Kabir da tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya ci zabe.

Kara karanta wannan

Nasara: Yan bindiga da yawa sun mutu yayin da sojoji suka daƙile hare-hare biyu a jihar arewa

Kotu ta yanke hukunci kan rusau a Kano

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan rusau da Gwamna Abba Kabir ya ke yi a jihar Kano.

Kotun ta rufe asusun bankunan gwamnatin jihar guda 24 har da na Babban Bankin Najeriya, CBN.

Wannan na zuwa ne bayan 'yan kasuwa da masu shaguna sun kai gwamnatin jihar kara kotu don neman hakkinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.