Neman Karbe Kujerar Abba Gida-Gida a Kotu Zalunci Ne Kawai, Malamin Musulunci

Neman Karbe Kujerar Abba Gida-Gida a Kotu Zalunci Ne Kawai, Malamin Musulunci

  • Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya zargi masu neman ganin bayan Abba Kabir Yusuf daga kan kujerar mulki da zalunci a Kano
  • Malamin musuluncin ya ce da aka yi zaben 2023, ta tabbata cewa jam’iyyar NNPP ta yi galaba a kan APC da ke kan mulki a lokacin
  • Shehin ya ce shi ma Abba ya yi irin na sa kuskuren da ya shiga ofis, amma haka bai bada dama a tsige shi da sunan shari’ar zabe

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi magana a kan abubuwan da ke faruwa a jihar Kano inda ake shari’ar zaben gwamna.

Shehin malamin ya yi wani jan hankali wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook lura da yadda shari’ar zaben Kano ke tafiya a yau.

Kara karanta wannan

"Muna Fatan Nasara": Hadimin Abba Ya Magantu Yayin Da Kotun Koli Ke Shirin Fara Zama Kan Shari'ar Kano

Abba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Hon Salisu Muhammad Kosawa
Asali: Facebook

Malamin addinin musuluncin ya ce a ra’ayinsa, kokarin lauyoyin jam’iyyar APC na karbe mulkin Kano zalunci kurum ake shirin yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuskuren da Gwamnatin Abba tayi a Kano

Babban malamin yake cewa amma duk da abin da yake faruwa, shi ma gwamnan ya fara mulkinsa da kuskure da aka rantsar da shi.

Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce ‘yan jam’iyyar APC sun yi barci ne har NNPP ta doke su a zaben Kano da aka shirya a farkon shekarar nan.

Bayan haka, a bidiyon an ji shi yana gargadin magoya baya cewa abin da ke faruwa a kotu ba zai bada lasisin zagin malaman addini ba.

Ibrahim Aliyu Kaduna a kan Abba Kabir Yusuf

"Ni ne ‘dan goyon bayan Abba Gida Gida domin an yi zabe a Kano, Abba Gida Gida ya ci, ya kada wadancan.

Kara karanta wannan

Ba yau ne farau ba: Kwankwaso ya yi tir da Sojojin da su ka kashe mutane a Kaduna

Mugunta ce kawai yanzu ake so ayi wa Abba Gida Gida a karbe kujerarsa, mugunta ce, kuma ni ban yarda ba.
Duk da shi ma rushen-rushen da ya yi…ba ka fara zamaninka da sharri. Na yarda ya yi kuskure, a hukunta shi a kan kura-kuransa.
Amma a karbe kujerarsa, zalunci ne. Wannan ra’ayi na ne, ina yi fadi, kai ma za ka iya fadi."

- Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna

Abba ya yi Rusau a Kano

An ji rushe-rushen da gwamnatin jihar Kano ta rika yi bayan tafiyar Abdullahi Umar Ganduje ba daidai ba ne a ra’ayin wasu da-dama.

Gwamnatin NNPP ta ce an saba doka wajen yin wasu gine-gine, amma APC ta ce abubuwan da ke faruwa alhalin 'yan kasuwa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng