Atiku Abubakar Ya Bayyana Gaskiya Kan Shirin Haɗa Maja Da Kwankwaso Da Wasu Jam'iyyu 6

Atiku Abubakar Ya Bayyana Gaskiya Kan Shirin Haɗa Maja Da Kwankwaso Da Wasu Jam'iyyu 6

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa a halin yanzu tana kokarin farfaɗowa bayan kashin da ta sha a zaben shugaban ƙasa na 2023
  • Babbar jam'iyyar adawa ta kasa ta faɗi haka ne yayin da take musanta rahoton cewa ta fara shirin haɗa maja da wasu jam'iyyu
  • Mai magana da yawun PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya fayyace gaskiya kan matsayar jam'iyyar yayin da take shirin tunkarar 2027

FCT Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ƙasa ta nesanta kanta da jita-jitar haɗa maja da wasu jam'iyyun adawa.

Idan baku manta ba, an tattaro cewa PDP da New Nigerian Peoples Party (NNPP) sun fara yunkurin curewa wuri ɗaya domin tunkarar babban zaɓe mai zuwa a 2027.

PDP ta musanta rahoton maja.
Atiku Ya Yi Magana Kan Shirin Hada Maja da Kwankwaso da Wasu Gabanin 2027 Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Facebook

An ce jam'iyyun sun fara wannan tunanin ne biyo bayan kashin da yan takararsu na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da Rabiu Kwankwaso, suka sha a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

An kuma: Yan bindiga sun kai sabon hari, sun yi garkuwa da ɗaliban jami'ar tarayya a arewa

Jam'iyyu bakwai da suka shiga majar sun raɗa wa kansu suna da, 'Coalition of Concerned Political Parties (CCPP)’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron tattaunawar ya gudana ne ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, 2023 a sakateriyar jam'iyyar SDP, kuma wakilan kowace jam'iyya sun halarta.

Menene gaskiyar wannan labari?

Da yake martani kan batun a wata hira da jaridar Vanguard ta wayar salula ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba, sakataren watsa labaran PDP, Debo Ologunagba, ya musanta shiga tattaunawar maja.

Da aka tambaye shi da gaske PDP ta shiga zaman tattauna yadda za a haɗa karfi da ƙarfe wuri ɗaya a tsagin adawa, Ologunagba ya ce:

“PDP ita ce jam’iyya mafi tsari da dimokuradiyya da ta wanzu a Najeriya har yau. Mafi yawan sauran jam'iyyun siyasa duk asalinsu daga PDP suka fito. Ba mu shiga kowace tattauna da sunan haɗa maja ba."

Kara karanta wannan

An yi rashi: Tsohon sakataren NUPENG, Frank Kokori ya yi bankwana da duniya yana da shekara 80

"Ko da ma akawai abu mai kama da haka, ya zarce ikon kwamitin gudanarwa ya yi gaban kansa sai da sahalewar kwamitin zartarwa na PDP ta ƙasa."

Ministan Shugaba Tinubu Ya Fice Daga Jam'iyyarsa

A wani rahoton kuma Ministan wutar lantarki a Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da aniyarsa ta komawa jam'iyyar APC.

Adebayo Adelabu, wanda ya riƙe tutar takarar gwamnan Oyo a inuwar Accord Party a zaben 2023, ya tabbatar da haka a wata wasiƙa da ya aiko wa Legit Hausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262